Accessibility links

'Yan Banga Sun Yanka Kunnen Dan Bindiga Sun Tilasta Shi Ya Cinye

  • Ibrahim Garba

'Yan bangan Fararen Hulan JTF suna anfani ne da kulake da sanduna da makaman da aka sarafa cikin gida suna sintiri a kan titunan Maiduguri, Najerya.

'Yan Bangar da ake kira Fararen Hulan JTF sun yanka kunnen wani dan bindiga sun tilasta shi ya ci ya hadiye

Wani dan garin Michika na jihar Adamawa ya shaida ma Muryar Amurka (VOA) cewa ‘yan bangar sa kai sun kai samame a garin Michika na Jihar Adamawa su ka kama wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne da su ka ketaro daga jihar Borno.

Wakilinmu na shiyyar Adamawa, Ibrahim Abdul’aziz ya ruwaito ganau din na cewa ‘yan goran sun taho ne daga Maiduguri su ka ce su na da bayanin cewa wasu ‘yan Boko Haram da su ka gudo daga Bama sun buya a garin. Don haka idan su na zargin mutum da zama dan Boko Haram sai su ba shi Alkur’ani ya rantse. Idan ya rantse sai su bar shi. Akwai wanda su ka buge shi cikin kuskure su ka ba shi kudi ya je ya yi jinya. To amma akwai kuma wanda su ka fahimci cewa shi dan kungiyar ce sosai sai su ka yanke kunnensa su ka ba shi ya ci ya hadiye.


Ibrahim ya ce ‘yan goran sun mika wadanda ake zargin su goma sha daya ga sojoji, su kuma sojojin sun wuce da shida daga cikinsu zuwa Maiduguri, biyar kuma zuwa Bataliyar Soja ta Musamman da ke tabbatar da tsaro a yankin Mubi da kewaye. Kakakin Rundunar ‘Yansandan Jihar Adamawa DSP Mohammed Ibrahim ya tabbatar cewa an baza jami’an tsaro cikin daji don zakulo ‘yan bindigar da su ka kashe wasu jami’an tsaro biyu a Karamar Hukumar Gombi.
XS
SM
MD
LG