Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 20 A Najeriya, Wasu Kuma Sun Jikkata


Rundunar 'yan sanda
Rundunar 'yan sanda

Rudunar ‘yan sandan jihar Filato ta ce, akalla mutane 20 ne suka mutu wasu kuma suka samu raunuka a harbin bindiga ranar Alhamis bayan da wasu ‘yan bindiga su ka kai hari a wasu kauyuka biyu a jihar, inda ake yawan samun tashin hankali tsakanin makiyaya da manoma.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Filato, Alfred Alabo, ya ce an kai hare-haren ne da sanyin safiyar Alhamis, inda wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka kai hari kauyen Tagwam Lawuru, inda suka harbe mutane 17 suka kashe wasu uku a kauyen Layowok da ke kusa.

Gawan wani da aka kashe.
Gawan wani da aka kashe.

“Sakamakon hare-haren, wasu mutane da dama sun samu raunuka daban-daban na harbin bindiga,” in ji Alabo a wata sanarwa da ya fitar, inda ya bukaci a kwantar da hankula tare da yin alkawarin kamawa tare da hukunta wadanda suka aikata laifin.

Yawan tashe-tashen hankula a yankin, ya samo asali ne daga kabilanci da addini tsakanin Fulani makiyaya Musulmai da manoma Kiristoci.

Sai dai masana da ’yan siyasa da dama sun ce sauyin yanayi da fadada noma na haifar da gasa ga filaye da ke jefa manoma da makiyaya cikin rikici ba tare da la’akari da addini ko kabilanci ba.

~ REUTERS

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG