Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 3 a Harin Sokoto


‘Yan bindiga sun yi barin wuta a garin Tunga da ke karamar hukumar Illela a jihar Sokoto, lamarin da ya sa mazauna garin gudun tsira da rayukansu zuwa makwabtan garuruwa.

Wani hari da wasu mutane dauke da makamai suka kai garin Tunga a kusa da Gaidaw da ke cikin karamar hukumar mulkin Illela, mai iyaka da Birni N'Konni a jamhuriyar Nijer ya yi sanadiyyar kisan mutane 3, wasu 5 kuma suka jikkata.

An garzaya da hudu daga cikin wadanda suka jikkatan zuwa asibiti a jihar Sokoto don a yi musu jinya saboda su na cikin matsanancin hali.

Maharan dai sun yi wa jama'ar garin ruwan harsasai ba tare da wani dalili ba. Daya daga cikin wadanda suka jikkata a harin, da ya so a sakaya sunansa, ya ce da misalin karfe 7 na maraice harin ya auku sai dai maharan basu yi garkuwa da wasu ba amma sun balle wani shago suka kwashi kayayyaki da kuma kudi.

Karin bayani akan: Gaidaw, jihar Sokoto, garin Tunga, Nigeria, da Najeriya.

Al’ummar garin dai sun kwana cikin yanayin tashin hankali da fargaba bayan da suka fuskanci wannan mummunan lamari a garuruwan da ke kusa da garin Tunga. A halin da ake ciki, jama’ar sun gudu zuwa garin Gaidaw bayan faruwar lamarin.

Saurari karin bayani daga Harouna Mamane Bako:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00


Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG