Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Majalisar Dattijan Amurka Za Su Tunkari Myanmar Kan Kisan Kare Dangi


A jiya Laraba ne wasu ‘yan Majalisar Dattijan Amurka suka shirya tunkarar kasar Myanmar kan kisan kare dangi ga wata kabila, inda ‘daya daga cikin ‘yan jam’iyyar Democrat ya zargi shugaban masu rinjaye Mitch McConnell na kin aikata komai kan rikicin Rohingya saboda alakarsa da shugabar kasar, Aung San Suu Kyi.

Sama da shekaru 20 McConnell ke zama mutumin da yake gabatar da matakan takunkumi dake auna sojojin dake mulki, wanda daga karshe suka saki Suu Kyi daga ‘daurin talala kuma suka bari aka gudanar da zabe kuma jam’iyyarta ta lashe zaben a shekarar 2015.

A cewar sanata Dick Durbin, McConnell yaji, kuma duk muma munji a shekarun da suka gabata Suu Kyi ta nuna karfin hali, amma hakan ba zai sa muyi watsi da abin da yake faruwa yau a kasar da take bukatar shugabancinta.

‘Yan sa’o’i kafin nan, Durbin da sauran sanatoci 14 ciki harda ‘dan jam’iyyar Republican Johan McCain na Arizona da Marco Rubio na Florida sai kuma ‘dan Democrat Tim Kaine na jihar Virginia da Dianne Feinstein ta California, suka gabatar da wani kuduri dake Allah wadai da tashin hankalin da ya raba ‘yan kabilar Rohingya da wasu tsiraran kabilu daga gidajensu. suka kuma yi kira ga gwamnatin kasar ta ‘dauki matakan gaggawa na dakatar da duk wani tashi hankali.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG