Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Shi'a Sun Kara Kaimi A Fafutukar Ganin An Sake El-Zakzaky


Sheik El-Zakzaky

‘Yan kungiyar Shi’a almajiran Ibrahim Elzakzaky sun kaddamar da sabuwar zanga zanga don neman gwamnatin Najeriya ta ba da dama a kai malamin asibiti a kasar waje saboda yana fama da tsananin rashin lafiya.

Kakakin almajiran Elzakzaky a Abuja Muhammad Ibrahim Gamawa, yace albarusan da a ka harbe shi dasu a watan Disambar 2015 sun illata malamin har ma garkuwar jikinsa dake kare shi daga cutuka ta dakushe.

Tun da aka kama Elzakzaky daga gidansa a Gyellesu Zaria a shekarar 2015, jami’an tsaron Najeriya ke ci gaba da rike shi har lokacin da babbar kotun tarayya ta Abuja ta bada umurnin a sake shi.

Lauyan jami’an tsaron farin kaya Tijjani Gazali yace hukuma zata nazarci hukuncin Elzakzaky.

Akwai lokacin da masu zanga zanga suka balla babban kyauren shiga majalisar dokokin Najeriya domin nuna damuwar su ga yanda gwamnatin tarayya ke ci gaba da rike da shugabn nasu.

Yanzu dai za a jira a ga yadda takaddamar za ta kare yayin da kwanakin baya likitoci daga Iran su ka ziyarci Elzakzaky a inda yake zaune da matarsa Zinatdeen.

Ga karin bayani daga wakilin mu Saleh Shehu Ashaka:

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG