Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yansandan Israila Sun Kashe Wani Dan Eritrea Bisa Kuskure


Dan Eritrea da 'yansandan Israila suka harbe bisa kuskure .

'A Isra'ila 'Yansandan kasar sun harbe suka kuma kashe wani dan kasar Eritiriya wanda yake dakon safa a tashar mota shi da wani abokinsa bisa kuskure. Suna zaton wani ne da ake zargin ya kai hari a tashar motar. Al'amarin ya auku ne ranar Lahadi. Abokin nasa ya gayawa Muryar Amurka cewa sunji harbe harbe yayinda suke dakon motar kiya-kiya, kamar kowa suka ruga da gudu, amma da ya fito waje ya duba bai ga abokin nasa ba mai suna Hebtom Zerhom. Abokin nasa yace wani dan kasarsu ya gaya masa cewa "gashi can kwance a kasa, mutane suna dukansa, yana kokarin tashi amma 'Yansanda suna danneshi." Hoton bidiyo da aka dauka wurin ya nuna mutumin wanda aka jikkata shi sosai kwance jina-jina a tashar mota a wuri da ake kira Beersheba a kudancin Isra'ila. 'Yansandan sun dauka Zerhom wani ne da ake zargi a harin da aka kai a tashar inda maharin ya kashe wani sojan Isra'ila ya raunata wasu mutane 10. Abokin Zerhom wanda aka kashen ya gayawa wannan tasha cewa ya koma gun abokinsa, inda 'Yansanda suka yi masa tambayoyi gameda abokin nasa. Bayan da suka tattara bayanan, yace sai suka kai su dukkansu biyu wani asibiti, inda daga bisani aka gaya masa cewa abokinsa Zerhom ya cika. 'A Isra'ila 'Yansandan kasar sun harbe suka kuma kashe wani dan kasar Eritiriya wanda yake dakon safa a tashar mota shi da wani abokinsa bisa kuskure. Suna zaton wani ne da ake zargin ya kai hari a tashar motar. Al'amarin ya auku ne ranar Lahadi.

Abokin nasa ya gayawa Muryar Amurka cewa sunji harbe harbe yayinda suke dakon motar kiya-kiya, kamar kowa suka ruga da gudu, amma da ya fito waje ya duba bai ga abokin nasa ba mai suna Hebtom Zerhom.

Abokin nasa yace wani dan kasarsu ya gaya masa cewa "gashi can kwance a kasa, mutane suna dukansa, yana kokarin tashi amma 'Yansanda suna danneshi." Hoton bidiyo da aka dauka wurin ya nuna mutumin wanda aka jikkata shi sosai kwance jina-jina a tashar mota a wuri da ake kira Beersheba a kudancin Isra'ila.

'Yansandan sun dauka Zerhom wani ne da ake zargi a harin da aka kai a tashar inda maharin ya kashe wani sojan Isra'ila ya raunata wasu mutane 10.

Abokin Zerhom wanda aka kashen ya gayawa wannan tasha cewa ya koma gun abokinsa, inda 'Yansanda suka yi masa tambayoyi gameda abokin nasa. Bayan da suka tattara bayanan, yace sai suka kai su dukkansu biyu wani asibiti, inda daga bisani aka gaya masa cewa abokinsa Zerhom ya cika.

Sun je tashar ce domin sabunta takardun izinin zama a kasar.

XS
SM
MD
LG