Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Balarabe Ya Kai Hari Kan Sojan Israila


Firayim Ministan Israila Benjamin Netanyahu

Wani balarabe dauke da bindiga da wuka ya kai hari kan yahudawa a tashar motar safa jiya Lahadi a Beersheba.

Balaraben ya kashe sojan Isra’ila daya da raunana mutane goma kafin ‘yansanda su harbe shi har lahira.

Wannan dai shine harin jina-jina mafi muni a makonni biyu da Isira'ila da Falasdinawa suna kaiwa juna hare hare. Kawo yanzu an hallaka Yahudawa takwas da Falasdinawa arba’in da daya.

Cikin kankanin lokaci aka gano ko wanene wanda yayi harbin a tashar motar. Cikin wadanda suka jikkata har da wani dan kasar Eritrea da ‘yan sanda suka harbe bisa kuskure suna zaton shine dan bindiga na biyun.

An sami rahoton rikici a ranar Lahadi a birnin Hebron da ke gabar yammacin kogin Jordan, da kuma kan iyakar Isra’ila da Gaza.

‘Yansanda sun fara gina Katanga tsakanin garin Yahudawa na Armon Hanatziv da na Falasdinawa Jabel Mukaber da suke ta gabashin Kudus don kawo karshen rikicin.

XS
SM
MD
LG