Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Israila Sun Harbe Falasdinawa Biyu Har Lahira a Birnin Kudus


Sojojin Israila na musamman suna sintiri a tsakiyar birnin Kudus

Rikici tsakanin Yahudawa da Falasdinawa sai kara zafafa yake yi tare da samun hasarar rayuka

Sojojin Isra’ila sun harbe wasu su biyu da suka kai hari da wuka a daidai wannan lokaci da ake ta kai harin suka da wuka da harbi akan fararen hula da sojoji Yahudawa a birnin Kudus.

A harin farko a jiya Laraba, ‘yan sanda sun harbe wani mai kokarin sukar jami’in tsaro a wajen mashigar tsohon birnin na Kudus ba tare da wani Bayahude ya ji rauni ba.

Dayan kuma da ‘yansanda suka bayyana cewa dan ta’adda ne, sun ce ya soki wata mata ne a kusa da tashar shiga motocin safa safaya kuma yi kokarin shiga wata motar amma kafin nan aka harbe shi har lahira.

Wannan rikicin dai na faruwa ne a daidai lokacin da Isra’ila ke jigilar kai sojoji zuwa birane saboda taya ‘yan sanda shawo kan lamarin, wanda hakan ya ke dada tada kurar rikicin Isra’ila da Falasdinu.

XS
SM
MD
LG