Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Firayim Ministan Israila Yace Ashirye Yake Ya Gana da Shugaban Falasdinawa


Wani Bafalasdine yana jifan Yahudawa lokacin da suke fada tsakanin su

Ahmed Mansara wanda Israila ta zarga da sukan Yahudawa biyu kafin jami'an tsaro su harbeshi shi ne musabbabin takaddama ta baya bayan nan da ta taso tsakanin Yahudawa da Falasdinawa

Firayim Ministan Israila Benjamin Netanyahu yace a shirye yake ya gana da shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas da zummar kawo karshen tashin hankali tsakanin bangarorin biyu amma ya kara da cewa shugaba Abbas ya daina karerayi akan Israila.

Musamman Netanyahu ya bukaci Falasdinawa da su daina yada jita-jita cewa Israila na nufin kwace gabashin birnin Kudus inda masallacin al-Aqsa dake da mahimmanci ga musulmi yake wanda kuma Yahudawa suke kira Tudun Sujada.

Firayim Ministan ya kalubali Falasdinawa akan abun da ya kira babbar karya dake cewa dakarun tsaron Israila suna yiwa Falasdinawa wadanda suke kyautata zaton 'yan ta'ada ne kisan gilla. Yace gwamnatinsa na yin abun da kowace gwamnati zata yi da mutane dake dauke da wukake da masu yankan mutane da masu sare mutane da gatura suna kokarin kashe kowa suka gani akan hanya.

Musabbabin wannan takadda ta baya bayan nan shi ne wani yaro Bafalasdine dan shekara 13 mai suna Ahmed Mansarada da ya soki Yahudawa biyu da wuka ranar Litinin a birnin Kudus.

Hotunan yaron da aka nuna a talibijan an ga jini na fitowa daga kansa kana kafafunshi sun lankwade saboda mota ta takashi yayinda yake kokarin tserewa. Wasu da suke kusa da wurin sun yi ihu suna kiran 'yansanda su harbe yaron ya mutu..

Tun farko shugaba Abbas ya zargi Israila da yiwa yaron kisan gilla. Amma Israila ta nuna wani bidiyo jiya Alhamis inda Ahmed yana zaune a kan gadon asibiti da bandeji a kansa, yana cin abun kwalama tare da likitocin Yahudawa dake yi masa jinya.

Netanyahu yace irin wadannan kalamun dake tanada jijiyoyin wuya su ne suke harzuka Falasdinawa suna sukan mutane da wukake. Irin hare haren sun hallaka Yahudawa bakwai da raunata wasu fiye da 20. Saidai sojoji da 'yansandan Israila sun hallaka Falasdinawa 31.

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry yana shirin yin balaguro zuwa Gabas ta Tsakiya da nufin kawo karshen wannan tashin tashinar dake tsakanin Yahudawa da Falasdinawa ta hanyar shawo kansu su koma kan teburin tattaunawa.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG