Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Ta Sa'o'i 10 Ta Fara Aiki A Syria


Syria

A Syria,wata yarjejeniyar tsagaita wuta ta sa'o'i 10 da Rasha ta ayyana a birnin Aleppo, da yake-tsaka-mai-wuya, ta fara aiki.

Yarjejeniyar dai wani mataki ne da zai baiwa farar hula da 'yan tawaye baki daya damar su fice daga cikin birnin.

Babban hafsan hafsoshin Rasha Janar Valery Gerasimov, ya fada a farkon makon nan cewa an dauka ne domin kaucewa hasarar rayuka na babu gaira babu dalili, shiri da gwamnatin kasar ta Syria tayi na'ama da shi.
Akwai kuma wasu kofofi shida da farar hula zasu iya amfani da su domin fita daga birnin.
Duk da haka kungiyoyin 'yan tawayen a Aleppo, sunyi watsi da tayin da Rasha ta gabatar, sun zargi Rasha da kariya, sun kira shirin tsagaita wutar a zaman "farfaganda ce kawai". Rasha da Syria sun shirya irin wadannan tsagaita wutar a baya wadnada galibi basu sami nasara ba. Na baya bayan nan shine wanda suka ayyana a tsakiyar watan Oktoba, inda moticin dakon kaya dauke da kayan agaji daga MDD da kungiyar agaji ta kasa da kasa Red Cross, suka yi ta dako akan iyakar kasar Turkiyya na tsawon makonni, suna jiran tabbacin suna iya wucewa.
MDD tace kimanin farar hula dubu 250 suke matukar bukatar kayan masarufi cikin gaggawa a gabashin binrin Aleppo, da wasu daruruwa wadanda suke bukatar kulawar likitoci wadanda suke bukatar an dauke su daga yankin.

XS
SM
MD
LG