Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Ce Sabuwar Ranar Dimokaradiyya A Najeriya


Yau ne sabuwar ranar dimokradiyya a Najeriya, ranar da za’ayi bukukuwan rantsar da shugaba Muhammadu Buhari a wa’adi na biyu bayan da aka rantsar dashi a ranar 29 ga watan Mayu da ya gabata.

An gayyato shugabannin kasashen duniya daban-daban da jakadun ‘kasa da ‘kasa domin taya Shugaba Buhari murna.

A lokacin da shugaba Muhammadu Buhari yake yakin neman zaben wa’adi na biyu ya kara nanata cewa “Alkiblar wa’adi na biyu kamar na farko ne, shine yaki da cin ranci da rashawa, samar da tsaro da farfado da tattalin arziki”

Wannan bayanin dai shine yadan kara bada haske da nuna alkibla akan bayanan da gwamatin shugaba Muhammadu Buhari za ta yi ranar 12 ga watan Yunin shekarar 2019.

Inda ake sa ran zai fayyace dallah-dallah canje canje ko garanbawul da wannan fannonin zasu samu domin tabbatar da yaki da cin ranci da rashawa da matsalar tsaro, matsalar da al’umma da dama suke gani cewa tana ci gaba da tabarbarewa, duk da makudan kudade da gwamnatin ke kashewa wajen inganta tsaro a Najeriya.

Wannan bikin da za a yi yana da muhimmanci domin gwamnati zata kaddamar da 12 ga watan Yuni ko wacce shekara a matsayin ranar dimokaradiyyar Najeriya.

Ga Umar Farouk Musa da Karin bayani:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00

Facebook Forum

Zauren VOA Hausa #EndSARS

Zauren VOA Hausa #EndSARS Kashi na Biyu 03
please wait

No media source currently available

0:00 0:18:31 0:00
Karin bayani akan #ENDSARS: Zanga Zangar Kyamar Gallazawa Al’umma Da Yan Sanda Ke Yi

Rayuwar Birni

Rayuwar Birni: Hira da Aliyu Danlami mai sayar da furanni a Abuja
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:49 0:00
XS
SM
MD
LG