Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za Mu Ci gaba Da Hulda Da Kamaru - Amurka


Shugaban Kamaru, Paul Biya a New York, Satumba 22, 2016.

Kalaman na Jakadan Amurka, na zuwa ne bayan da rahotannin suka nuna cewa gwamnatin Amurka za ta rage Dala miliyan 17 na tallafin da take ba Kamaru na kayayyakin soji.

Duk da cewa ta sanar da shirin rage irin taimakon sojin da take ba kasar Kamaru, saboda zargin cin zarafin bil Adama da ake yi a kasar, wasu jami’an gwamnatin Amurka, sun ce, kasar za ta ci gaba da hada kai da kasar ta Kamaru ta fuskar tsaro.

Sai dai dakarun na Amurka, sun ce babu wani farar hula da harin ya shafa.

Takaita irin taimakon da Amurkan ke bai wa kasar, zai iya kawo cikas ga yakin da ake yi da masu tsattsauran ra’ayi a yankin.

Jakadan Amurka, Peter Henry Barlerin, ya tabbatarwa da hukumomin na Kamaru cewa, Amurka ba za ta daina hada kai da kasar ba ta fuskar ayyukan tsaro, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya ruwaito jakadan yana fada, bayan wata ganawa da ya yi da Kakakin gwamnatin Kamaru Rene Emmanuel Sadi.

Kalaman na Jakadan Amurka, na zuwa ne bayan da rahotannin suka nuna cewa gwamnatin Amurka za ta rage Dala miliyan 17 na tallafin da take ba Kamaru na kayayyakin soji.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG