Accessibility links

Zaben Anambara: APC ta Yi Zanga Zanga a Oyo

  • Ibrahim Garba

Shugaban hukumar zaben Najeriya Prof. Attahiru Jega

A cigaba da nuna rashin yaddar ta da sakamakon zaben gwamnan jihar Anambara, jam'iyyar APC shiyyar jihar Oyo ta yi zanga-zanga

Babbar yam'iyyar adawa a Nijeriya, APC na cigaba da nuna rashin yadda da sakamakon zaben gwamna da aka yi a jihar Anambara, wanda su ka ce an yi makircin hana jam'iyyaru su ta APC nasara bayan ita ta fi karbuwa.

Masu zanga zangar, in ji wakilinmu a jihar Oyo Hassan Ummaru Tambuwal sun fito ne daga kananan hukumomi 32 na jihar, inda su ka yi maci daga Fadar Gwamnatin jihar zuwa hedikwatar hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) inda su ka nuna bacin ransu.

Shugaban riko na jam'iyyar a jihar Anambara Alhaji Alimi Isyaka wanda har ila yau kuma shi ya jagoranci zanga-zangar, ya ce sakamakon zaben jihar Anambara wofinta tsarin dimokaradiyya ne kawai.

Shi kuwa babban jami'in gudanarwwa na hukumar ta INEC da su ka tarar, Alhaji Rafiu Adebele ya ce la shakka zai kai koken nasu hedikwatar INEC din da ke Abuja.

XS
SM
MD
LG