Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zanga-Zangar Kin Jinin Gwamnatin Pakistan


Nawaz Sharif.
Nawaz Sharif.

Anyi kira ga masu zanga-zangar kin jinin gwamnati da su daina biyan haraji.

Wani babban shugaban 'yan hamayya a majalisar dokokin kasar Pakistan yayi kira ga masu zanga-zangar kin jinin gwamnati da su daina biyan haraji, kuma su daina biyan kudin wuta da gas har sai firai minista Nawaz Sharif yayi murabus.

Imran Khan ya lashi takobin cewa shi da malamin addinin Islama mai farin jinin jama'a Tahirul Qadri za su matsawa Mr. Sharif yayi murabus a wannan mako. Sun yi zargin cewa bara da aka yi zabe an yi magudi, shi ya sa jam'iyar Mr.Sharif ta yi nasara.

Dubban masu zanga-zangar kin jinin gwamnati sun cika titunan birnin Islamabad a kwana na biyu a jere a jiya lahadi. Hukumomi sun karfafa tsaro a manyan unguwannin birnin domin hana barkewar tashin hankali a lokacin zanga-zangar.

Ministan kudin kasar Pakistan Ishaq Dar da ministan yada labarai Pervaiz Rashid sun shaidawa manema labarai a jiya lahadi cewa gwamnati a shirye ta ke ta zauna da 'yan hamayya ta tattauna da su akan bukatun su na neman wasu sauye-sauye game da yadda ake zabe a kasar.

XS
SM
MD
LG