Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZANU-PF Ta Samu Rinjayi A Majalisar Dokoki A Zinbabwe


Shugaban Zimbabwe Emmerson Mngangwa
Shugaban Zimbabwe Emmerson Mngangwa

Wani bangaren sakamkon zaben da ya fito yau Laraba a hukumance ya nuna jami’iyar ZANU-PF mai mulki a kasar Zimbabwe ta lashe kujerun majalisar dokoki masu yawa, lamarin da zai kai ta ga samun rinjayi a majalisar.

Wasu alkalluma da hukumar zaben Zimbabwe ta fitar na nuna ZANU-PF ta lashe kujerun majalisar dokokin 109 a cikin kujeru 210.

Sai dai yanzu ne ake shirin bayyanar da sauran yan takarar da suka lashe kujerun majalisar.

Masu sa ido a kan zaben na tarayyar Turai sun ce ba a gudanar da zaben bisa adalci ba, suna fadin cewa an tsorata jama’a kana akwai rashin yarda game da ayyukan hukumar zabe da kuma rashin adalcin ma’aikatun jarida.

Kimanta zaben da Tarayyar Turai tayi wacce kuma take neman dalilin da yasa aka jinkirta fidda sakamakon zaben shugaban kasa, wani abu ne da aka dauka mai muhimmanci wurin tabbatar da ko Zimbabwe ta maido da martabarta a idon duniya, lamarin da zai kai ta ga samun bunkasar tattalin arziki.

Har iyau ana ci gaba da kirga kuri’ar zaben shugaban kasa kuma ana sa ran za a fitar da sakamakon zuwa karshen wannan mako.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG