Jam'iyar PDP Shiyyar Arewa Maso Gabas Ta Yi Taron Sulhu

Bakin ‘ya’yan jam’iyyar PDP shiyyar arewa maso gabashin Najeriya, ya zo daya da batutuwa da suka rage kimarta a idon masu kada kuri’a da ya kai ta ga shan mummunan kaye daga jam’iyya mai jihohi hudu zuwa biyu a shiyyar.

Jam’iyar PDP ta bada bayanin haka ta bakin shugaban kwamitin sasantawa da shiga tsakani kuma gwamnan jihar Taraba Arc. Darius Dickson Ishaku a zaman babban taron ta da kaddamar a Yola fadar jihar Admawa gabannin babban taron ta na kasa da shirye shiryen shiga zabubbukan shekarar 2019.

Da yake jawabi a taron shugaban jam’iyar PDP ta kasa shiyyar arewa maso gabas, Jakada Emmanuel Njuwa ya ce daga cikin batutuwa da suka sa PDP ta sha kaye akwai gunaguni game da yadda ake tafida lamura daga sama wanda ya sa ‘yan jam’iyar suka juya mata baya lokacin zabubbuka.

Batun da ya fi daukar hankulan mahalarta taron sune yadda jam’iyar zata kauda rashin adalci da dauki dora lokacin zaben fidda da gwani da rashin kamanta gaskiya wajen gudanar da lamuran jam’iyar wanda shugaban rikon kwarya na PDP jihar Adamawa Hon Mohammed Alkali Imam ya ce na bukatar a magance su cikin gaggawa.

Bayanin bayan taro da Sanata Grace Bent ta bayar ya nuna jam’iyar PDP shiyyar arewa maso gabas zata karawa mata da matasa guraben da za a rika damawa da su a harkokin shiga takara da gudanar da jam’iyar.

Saurari Karin bayanin rahoton Sanusi Adamu.

Your browser doesn’t support HTML5

Jam'iyar PDP Shiyyar Arewa Maso Gabas Ta Yi Taron Sulhu