Ana Makokin Fashewar Bam Din Kabul Ta Kasar Afghanistan

Jana'izar Wasu Da Suka Mutu a Harin Kunar Bakin Wake a Kabul Lokacin Wata Zanga Zanga

Kasar Afghanistan ta bada hutun zaman makoki a duk fadin kasar don jimamin mutuwar mutane akalla 80 da kuma jikkata sama da 200 a harin bam din kunar bakin waken da ya tarwatse a tsakiyar dandazon masu zanga zangar lumana a Kabul.

Kamar yadda Ministan cikin gidan kasar ya bayyana a jiya Asabar. Inda yace ‘yan kunar bakin wake ne guda 3. Na farko ya tada kansa cikin jama’ar, na biyu kuma ya tada kansa shi kadai bisa kuskurensa.

Sai kuma mutum na 3 da jami’an tsaron da ke lura da masu zanga-zangar suka bindige kafin ya kai ga tada nasa bam din. Tuni dai ‘yan kungiyar ta’addar ISIS suka dauki alhakin kai harin na jiya.

Sanarwa ISIS din a shafin intanet tace, wannan harin gargadi ne ga ‘yan kabilar ta Hazaras din da yawancinsu ‘yan shi’a ne, inda suka ce suna musu kashedin da su daina hada kai da gwamnatin Syria ana yakarsu.

Ko a yau din nan ISIS sun kai harin Bam din da ya kashe mutane 12 ya jikkata 25, a wani shingen tsaro da ke wata unguwar ‘yan shi’a a Iraqi.