Malamai Kimanin 30 Aka Kashe A Jihar Borno

Shugaban kungiyar malaman firamare a Jihar Borno, Comrade Bulama Abiso, yace hare-haren 'yan bindiga sun kashe malamai kimanin 30 a fadin jihar
An kashe malaman makarantun firamare da na sakandare kimanin 30 a Jihar Borno a hare-haren da 'yan bidniga suka rika kaiwa a cikin jihar a 'yan watannin nan,

Shugaban Kungiyar Malaman Makarnatun Firamare a Jihar Borno, Comrade Bulama Abiso, shi ne ya bayyana hakan a wajen bukin ranar tunawa da malamai ta duniya da aka gudanar a garin Maiduguri.

Ya roki gwamnatin jihar Borno da hukumomin tsaro da su tabbatar da daukar karin matakan kare malamai, wadanda suke sadaukar da rayukansu domin koyar da dalibai a jihar.

haka kuma, Comrade Bulama Abiso, ya roki gwamnati da ta duba batun albashi mafi kankanci da ya kamata a rika biyan malamai, yana mai fadin cewa a hukumance, su na goyon bayan matakin tacewa da tabbatar da malaman makarantun da gwamnati take aiwatarwa.

Wakilin Sashen Hausa, Haruna Dauda Biu, ya aiko da cikakken bayanin wannan buki a bayan ya tattauna da shugaban kungiyar malaman.

Your browser doesn’t support HTML5

An Kashe malamai 30 A Jihar Borno Sakamakon hare-haren 'yan bindiga - 3:29