NIGER: Kungiyar HED TAMAT Ta Yi Shelar YinTakardu Kyauta Ga Al'umma

Wata kungiya da ake ce ma HED TAMAT mai fafutukar kyautata rayuwar a'umma ta gudanar da wata shela ta yi wa wadanda ba su da takardu rajista kyauta a yankin Agadez.

Mallakar takardu nada matukar muhimmanci kama daga takardun haihuwa, aure zama dan kasa da sauransu, musammamn a wannan zamani da kusan komai ke bukatar takardu domin tantancewa.

Ta dalilin haka ne wata kungiya mai suna HED TAMAT, ta yi amfani da ranar bikin lasar gishiri da aka gudanar domin yiwa jama’a rajistar takardu a kyauta, jama’a da dama sun bayyana ra’ayoyin su akan samun takardun musamman matafiya.

Aisa Dodo, ma’aikaciya a ma’aikatar yin takardu ta magajin gari, ta bayyana amfanin mallakar takardun kasa da na haihuwa da sauransu mai matukar amfani, musamman ganin yadda kasashen duniya ke kara daukar matakai kan shigi da ficen jama’a.

Ga rahoton Tamar Abari.

Your browser doesn’t support HTML5

NIGER: Kungiyar HED TAMAT Ta Yi Shelar YinTakardu Kyauta Ga Al'umma