Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ministan Tsaro A Nijer Ya Ce Gwamnati Zata Bada Bayanai Kan Harin Da Aka Kai


Wasu sojojin jamhuriyar Nijer da na Amurka sun hallaka yayinda wasun su suka yi batan dabo bayan da suka fada tarkon ‘yan bindiga a jiya a wani wurin dake arewacin jihar Tilaberi kan iyakar Nijer da Mali lokacin da suke aikin sintiri.

A yayin da suke kokarin cafko wasu ‘yan bindiga da suka kai hari sojojn na jamhuriyar Nijer da wasu Amurkawa dake basu horo suka yi arba da wasu ‘yan takife dake dauke da manyan bindigogin yaki inda suka yi masu kwanton bauna wato kan iyakar Mali da jamhuriyar Nijer.

Rahotanni sun bayyana cewa an kwashe okaci mai tsawo ana musayar wuta tsakanin bangarorin biyu, kafin daga karshe ‘yan ta’addar suka yi nasarar hallaka sojojin Amurka da na jamhuriyar Nijer.

Honorable Karimu Burema, na daga cikin wakilan al’ummomin jihar Tilaberi, a majalisar dokokin kasa ya bayyana cewa sojojin Amurka uku suka hallaka guda kuma ya ji mummunan rauni, sai kuma guda biyu na jamhuriyar Nijer, ya kuma kara da cewa an hallaka dabbobi da dama, amma ‘yan ta’addar sun arce da mutanen su da suka mutu da kuma wadandasuka jikkata.

Ministan tsaro na jamhuriyar Nijer, Kallla Musa, wanda ya tabbatar da afkuwar wannan hari ya kara da cewa kawo yanzu basu kammala harhada bayanai ba, amma gwamnati zatafitar da sanarwa a karshen taron majalisar koli mai kula da harkokin tsaro da za a gudanar a karkashin jagorancin shugaba Mahamadou Issoufou, a yammacin yau Alhamis.

Wannan kazamin hari ya faru ne a lokacin da kasashen kungiyar hadin gwiwa mai kokarin yaki da ta’addanci ta fara aiki a fagen daga, saboda haka shugaban ‘yan kwamitin ‘yan majalisar dokoki masu kula da sha’anin tsaro Muhamman Asa, ya kara jaddadawa askarawan kasar Nijer, da gwamnatin kasar goyon baya.

Wakilin muryar Amurka a yamai Sule Mumuni Barma nada Karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:28 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG