Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NIGER: Malaman Makaranta 'Yan Kwangila Sun Yi Kira Ga Gwamnati


Malaman makaranta ‘yan kwantiragi a jamhuriyar Nijer, sun yi kira ga gwamnati da ta yi kokarin biya musu bukatun su ta yadda za su ji dadin kama aiki cikin tsanaki.

Yayin da aka kama karatu a daukacin makarantun boko dake jamhuriyar Nijer, malaman makaranta ‘yan kwantiragi sun koka akan wasu daga cikin matsalolin da suka addabe su duk da cewa kungiyar malaman ta bayyana cewa sun koma bakin aiki.

Malam Ya’u Abdu, shine magatakarda na kungiyar malaman reshen Damagaran, ya bayyana cewa sun kama aiki ba tare da musayar yawu da gwamnati ba duk kuwa da cewa basu san yadda lamarin zai kasance a nan gaba ba.

A daya banagren kuma rahotanni sun bayyana cewa an fara biyan malaman hakkin su, ko wannan korafi da suke ba gajen hakuri bane daga garesu?, tambayar da wakiliyar sashen Hausa na muryar Amurka Tamar Abari ta yiwa Malam Ya’u, ke nan inda ya bayyana cewa wata daya kacal aka biya su duk da cewa matsalolin su nada tarin yawa.

Magatakardar kungiyar malaman makarantar ya kara da cewa lallai idan gwamnati bata dauki wani mataki ba kungiyar zata shiga takun saka tsakanin ta da gwamnati.

Malaman sun bayyana cewa koda aka ira iyayen yara da su tura yaransu makarantu domin ci gaba da daukar darussa, ba’a samar masu da kayan aiki ba, kuma babu malamin da zai sa kudin say a sayi kayan aiki tunda shugaban kasa ya ce akaranta kyauta ce.

Iyayen yara sun nuna rashin jin dadin su da kuma kira ga malaman da su taimaka domin ganin an sami maslaha da kuma tarbiyya a tsakanin daibai.

Daga Damagaran Tamar Abari, ta aiko mana da wannan rahoton.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:44 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG