Pompeo Yace A Taimakawa Venezuela

Pompeo a Majllisar Dinkin Duniya

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya yi kira ga kasashen duniya da su taimakawa mutane Venezuela kuma su amince da gwamnatin wucin gadin kasar karkashin jagorancin Juan Guaido yayin da yake fafatawa da shugaba Nicholas Maduro.

Babban jami’in diflomasiyar Amurka ya fadawa wani taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a jiya Asabar cewa yakamata a magance matsalolin taimako da kasar Venezuela ta fada a ciki.

Yace muna nan ne mu yi kira ga duk kasashen duniya su taimakawa tsarin damokaradiyar al’ummar Venezuela a kokari da suke yi su kwace ‘yancinsu a hannun tsohon shugaban Maduro da ya mayar da kasar ta ‘yan banga. Matsalolin taimako da kasar ke fama da ita tana bukatar daukar mataki yanzu.

Pompeo ya zargi Rasha da China da yunkurin marawa Maduro baya, alhali kuwa babu wata kasar da tayi wani kokari a kan batun bukatar da Venezuela ke nema sai Cuba kadai.