Shugaban kasar Saliyo ya ayyana dokar ta bace a kasar saboda yawan yiwa mata fiyade da kuma cin zarafin jima’ai da ya dabaibaye kasar.
WASHINGTON DC —
Julius Maada Bio yace duk wanda aka same shi da laifin lalata da kananan yara za a yanke masa hukuncin daurin rai-da-rai.
A shekarar da ta gabata an samu labarin aikata laifukan fiyade da cin zarafin jinsi dubu takwas a kasar Saliyo, lamarin da ya hada da kananan yara.
Ainihin adadin aikata laifukan ya haura abin da aka tattara, amma tattauanawa a kan batun laifukan cin zarafin jima’I tamkar wani babban abin ki a kasar dake Afrika ta Yamma.
Da yake ayyana dokar ta bacen, shugaban Bio yace a matsyin mu na kasa yakamata mu tashin haikan mu magance wannan mummunar dabi’ar.
Yace asibitotcin gwamnati zasu kula da lafiyar wadanda aka ci zarafinsu a kyauta.