Za a Rufe Wuraren Hakar Ma’adinai A Najeriya Don Yakar Ta'addanci

Gwamnatin Nigeria ta ba da umurnin hana hakar zinari da sauran albarkatun ‘kasa a jihar Zamfara tare da haramta shawagin jiragen sama a sararin samaniyar jihar A kokarin yaki da ta’ adds ci ya yayi kamari a jihar.

A wata hira da wakilin Muryar Amurka a Abuja mai baiwa Shugaban ‘kasar shawara a sha’anin tsaro Janar Mohammad Babagana Monguno (Rtd) ya yi karin bayani akan dalilan da suka sa aka hana hakar zinari.

A cewarsa, rufe wuraren hakar ma’adanai na da muhimmanci domin babbar matsala ce da ta shafi ta’addanci.

Janar Monguno ya amsa cewa wannan matakin zai kawo sauki ga satar dalibai da ake yi domin an danganta ta satar mutane, hakar ma’adanai da garkuwa da mutane ana neman fansa.

Ya kara da cewa masu hakan ma’adanai suna samun kudi mai yawa da suke harkokin shiga da makamai cikin kasar kamar yadda aka yi a wasu kasashen.

Ya ce sukan yi alaka da ‘yan Boko Haram saboda hanyar samun kudi ne mafi sauki kamar ta miyagun kawayoyi da ke ba su karfi da samu, don haka suka shiga garkuwa da mutane don neman fansa.

A saurari hirar ta su cikin sauti daga Umar Farouk Musa:

Your browser doesn’t support HTML5

Za a Rufe Wuraren Hakar Ma’adinai A Najeriya Don Yakar Ta'addanci