Jami'an kiwon lafiya a Amurka sun ce an gano mutum na farko da ya harbu da sabon nau'in cutar coronavirus na Omicron a California.
Yayin da iyalai da dangin mutane kimanin 40 da suka rasa rayukansu, galibinsu daliban makarantar Islamiyya, sanadiyyar hadarin jirgin ruwa na kwale-kwale a garin Bagwai na jihar Kano, gwamnatin jihar tace zata kafa kwamitin bincikar yadda al’amarin ya faru.
Sanar da sabon tsarin aikin kwanaki hudu a mako da gwamnatin jahar Kaduna ta yi ya jawo cecekuce har ma kungiyar Kiristoci ta Kasa CAN, reshen jahar Kaduna na cewa akwai lauje cikin nadi game da sabon tsarin aikin.
Shugaban kasar Nijer Mohamed Bazoum ya gana da shuwagabanin kungiyoyin addini inda ya bukaci gudunmowarsu wajen neman hanyoyin warware matsalar tsaron da ta addabi kasar da makwaftanta.
A Najeriya karancin samun wutar lantarki na tilasta wasu asibitoci na Jihohin da ke makwabtaka da Jamhuriyar Nijar tura gawarwakin zuwa kasar domin kar su lalace saboda rashin sanyi a wuraren ajiye su.
Fiye da shekaru shida bayan majalisar dokokin Najeriya ta amince da kudurin dokar dake bada kariya ga iyalai, musamman mata da yara, daga dukkanin nau’ukan cutarwa, har yanzu masu ruwa da tsaki na fafutukar ganin gwamnatin jihohin sun kafa tare da zartar da samfurin wannan doka a jihohin su.
Al’umomin Unguwar Tirwun da na sashen rukunan Jamiar Abubakar Tafawa Balewa a wajen Birnin Bauchi, sun gudanar da zanga zanga da kuma datse babbar hanyar data wuce Maiduguri,a wani mataki na kin amincewa da assasa Kamfanin tara iskar gas da Kamfanin mai suna Action Energy ke yunkurin ginawa.
Hukumar gidan gyara hali dake jahar Filato ta tabbatar da hari da ‘yan bindiga suka kai wa gidan yari.
Bayan Isar Alhaji Aliyu Mustafa Sokoto, shugaban Sashen Hausa na Murya Amurka zuwa Accra, ya fara da ziyarar tashar talabijin mai suna Hijra TV a ranar Asabar, inda ya samu gagarumin tarbo daga shugaban tashar, Abdul Razak Toure da ma aikatan tashar.
A karshe dai gwamnatin jahar Kaduna ta sanar da bude hanyoyin sadarwar da ta rufe na kusan watanni biyu sai dai ta ce sauran dokokin da aka sa su na nan ba a janye su ba.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) jiya Jumma'a Jumma'a ta ayyana nau'in B.1.1.529 da aka gano a Afirka ta Kudu a matsayin SARS-CoV-2 , ta na mai cewa nau'in yana iya yaduwa cikin sauri fiye da sauran nau'ikan.
Gwamnatin Najeriya ta ce za ta yi amfani da shawarar da Asusun Lamuni na IMF ta ba ta kan cire tallafin man fetur a watan fabrairu na shekara mai zuwa, sai dai da sharuda.
A jamhuriyar Nijer Hukumar sadarwa wato CSC ta gargadi kafafen yada labarai akan maganar mutunta ka’idodin aiki don gujewa haddasa rudani a kawunan al’umma a irin wannan lokaci na fama da matsalar tsaro.
Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta kama wani tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode a Legas.
A yayinda mayakan kungiyar boko haram ke cigaba da mamaye sassa daban daban a yankin Shiroro ta Jihar Neja dake arewa maso tsakiyar Nigeria, yanzu haka kuma gwamnatin jihar Nejan tace mayakan kungiyar Islama ta yammacin Afrika wato ISWAP na can ta fara aikin kafa wata daula a yankin Borgu.
A yayinda kwamitocin majalisar dokokin Jamhuriyar Nijer ke nazari akan kasafin kudaden shekarar 2022, shugabanin kungiyoyin fararen hula a nasu bangare sun fara binciken daftarin kasafin dake gaban majalisar.
Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta kama wani mutum da ta ce yana taimaka wa masu garkuwa da mutane ta wajen basu shawarwari.
A ranar Litinin din da ta gabata ‘yan sandan kwastam na kasar Italiya suka tarwatsa wata kungiyar ‘yan fatauci ta Najeriya da ta tilasta wa mata da dama yin karuwanci da bara a kan titunan kasar Italiya.
Domin Kari