An yi jana’izar wasu manoma 43 da aka kashe a wani hari da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne suka kai shi a kauyen Kwoshobe da ke karamar hukumar Mafa a jihar Borno.
Yayin da aka fara mayar da 'yan gudun hijirar jahar Borno zuwa garuruwansu, tawagar Hajiya Amina Mohammed, Mataimakiyar Shugaban Majalisar Dinkin Duniya, ta ziyarci sansanonin don ganin yadda ya kamata a taimaka a matakin kasa da kasa.
Helkwatan rundunar sojan Nigeria ta kaddamar da wani shiri da ake kira “Crocodile Smile” dan yaki da masu aikata laifaffuka ta yanar gizo da wasu miyagun ayyuka da al’umma ke aiwatarwa a duk fadin Nigeria.
Bayan wani hari da aka kaiwa tawagar Gwamnan jihar Borno Prof Baba Gana Umara Zulum a ranar jumma'a alumman jihar na ci gaba da bayyana ra'ayinsu a kan lamarin, da ma abin da ya shafi tsaro a jihar baki daya.
Gwamnan jihar Borno Prof. Babagana Umara Zulum ya bayyana alhininsa bisa mutuwar wasu jami’an tsaronsa 11 da suke rufawa tawagarsa baya tare da yin jinjina ga irin sadaukar da kansu da suka yi.
Jama'a sun yi cincirindo tare da daukar matakan kandagarki a wurin nadin sabon Sarkin Biu, Mai Martaba Mustafa Umar Mustafa.
A cikin wani hali na juyayi da alhini, an yi jana'izar marigayi Kanar Dahiru Ciroma da wasu 'yan bindigar da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne su ka kashe shi yayin da ya ke wani sintirin tabbatar da tsaro a Danboa, jahar Borno.
An gudanar da taron karawa juna sani tare da tuntuba a jihar Borno inda ake fama da matsalar tsaro, yayin kiyaye ranar zaman lafiya ta duniya.
Masarautar garin Biu ta ce sai ta kammala alnihin wannan babban rashin na babban sarkin yankin, Alhaji Mai Umar Mustapha Aliyu, kafin ta fara daukar shawara a kan wanda zai gaje shi bisa tsarin al’adun yankin.
A shirin da gwamnatin jihar Borno ke yi na tantance ma'aikatan kananan hukumomi 27 da ke jihar, gwamnatin jihar ta ce ta samu rarar fiye da N150m da ake biyan wasu ma'aikatan bogi fiye da dubu tara a kananan hukumomi 19.
Kakakin majalisar dokokin jihar Borno Hon. Abdulkareem Lawan ya ce a yanzu haka babu wani jami'in soja ko guda a karamar hukumar Guzamala dake arewacin Borno samakon hare- haren ‘yan ta’addan Boko Haram.
Gwamnatin tarayyan Nigeria ta kaddamar da wata hanyar samar da kayayyakin abinci ga 'yan gudun hijira ta hanyar amfani da jirgi mai saukan angulu inda za a dinga jefawa 'yan gudun hijiran ta sama a wuraren da baza a iya kaiwa ta kasa ba sakamakon matsalar tsaro da ake fama da ita.
Gwamnatin jihar Barno da ke Arewa Maso Gabashin Najeria ta kafa kwamiti mai wakilai 23 da zai yi aikin tantance ‘yan gudun hijiran Baga da yanzu haka ke karamar hukumar Kukawa sanadiyar tarwatsa garin da mayakan Boko Haran suka yi a ‘yan shekarun baya.
Gwamnatin jihar Borno ta soma maida mutanen da rikicin boko haram ya dai daita zuwa garuruwansu na asali da gina masu muhallin su sakamakon yan kwarya- kwaryan zaman lafiya da aka soma samu a wasu kyauyuka.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu gungun ‘yan bindiga da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne sun kai wasu hare-hare a karamar hukumar Damboa a jihar Borno da kuma garin Dapchi dake jihar Yobe.
An dawo da wadansu 'yan Boko Haram da iyalansu gida daga Jamhuriyar Nijar bayan sun bayyana niyarsu ta ajiye makamai su rungumi zaman lafiya.
Rundunar ‘Yan Sanda a jihar Barno, ta kame mutane 51 da ake zargi da aikata laifuka daban daban a fadin jihar.
Mannan matsalar ta sa mata da dama rasa mazajensu, inda hakan ya haifar da dubban marayu. Gwamnatocin da wannan ibtila'in ya shafa sun kai ziyara wadannan wurare don sannin halin da mutane suke ciki.
Domin Kari