Kaito, jahar Filato ta fara murmurewa daga tashin hankalin kwanan baya kenan sai kawai aka samu labarin kashe wasu masu sana'ar sayar da kayan miya su biyu. Wannan ya sake tuna ma al'ummar jahar Filato illar fitina, wacce idan ta tashi kwantar da ita sai an hada da matukar imani da tsoron Allah.
Yayin da duniya ke cikin wani yanayi na zaman dardar saboda dalilai dabandaban, yau ake hidimar zagayowa ta 100, ta tunawa da wadanda su ka sadaukar da rayukansu a yakin duniya na daya.
Ga dukkan alamu, hankalin 'yan Janhuriyar Dimokaradiyyar Kongo da ma na makwabtan kasashe zai sake tashi saboda sake bullar annobar mugunyar cutar nan ta Ebola. Tuni ma ta hallaka daruruwan mutane a wannan karon.
Hankalin 'yan Najeriya ya kwanta bayan da cikinsu ya duri ruwa saboda barazanar yajin aiki da kungiyar kwadago ta NLC ta yi amma kuma aka dace, gwamnatin tarayya da kuma kungiyar ta NLC su ka cimma jituwa.
Kallo ya koma Amurka, inda manyan jam'iyyun kasar wato da Republican (Rifofilikan) mai mulki da Democrat (Dimokarat) babbar jam'iyyar adawa, ke fafatawa a zaben gwamnoni da majalisa na rabin wa'adi.
A wani al'amari mai nuni da sarkakkiya, da kuma girman laifin da ake tuhumar mutanen 19 nan da ake zargi kashe Janar Idriss Alkali (murabus), kotun da ke shari'ar laifin a Jos ta ba da umurnin a cigaba da tsare su, babu bale, har sai ranar da za a cigaba da sauraren karar wato 10 ga watan 12.
Ganin yadda masu yinkurin haddasa fitina tsakanin mabambantan al'ummomi a Najeriya ke ta kokarin harzuka jama'a ta hanyoyi daban daban, ciki har da kashe-kashe, Rundunar sojin Najeriya ta sha alwasin ganin bayan irin wadannan mutane, a ko ina su ke kuwa.
A cigaba da fatattakar 'yan bindiga masu takura tsirarun jinsi da mabiya wasu addinai a Masar, sojojin kasar sun ce sun hallaka 'yan bindiga 19 masu alaka da kashe Kufdawa da aka yi ranar Jumma'a.
A wani al'amari mai daure kai, an tsinci gawarwakin 'yan mata biyu 'yan'uwan juna, kuma 'yan asalin kasar Saudiyya a wani kogi da ke birnin New York, a yayin da iyayensu su ka bukaci su koma gida Saudiyya.
Kufdawan kasar Masar sun sake ganin abin tashin hankali bayan da wasu 'yan bindiga, wadanda kungiyar ISIS ta ce 'ya'yanta ne, su ka kai hari kan wasu motoci dauke da wasu Kufdawa su ka hallaka bakwai daga cikinsu baya ga wasu 18 da su ka raunata.
Jama'ar kasa, musamman ma 'yan jarida, na cigaba da nuna alhininsu kan rasuwar daddiyar 'yar jarida, mace ta farko da ta zama 'yar jarida a Nijar, kuma tsohuwar shugabar Hukumar Sadarwa ta Nijar, Hajiya Maryama Keita.
An ce idan ka ga gemun dan'uwanka ya kama da wuta , to ka shafa ma na ka ruwa, don haka gwamnatin jahar Ekiti, ganin yadda ake ta samun tashe-tashen hankula tsakanin makiyaya da manoma a sassan Najeriya, ta kuduri aniyar sasanta tsakanin makiyaya da manoma a jahar.
A cigaba da kokarin kwantar da hankula da ake yi a Kaduna, Shugaban Najeriya da kansa, ya kai ziyarar ta'aziyya da kuma nuna goyon bayan matakan gaggawa da gwamna Nasiru El-Rufa'i ya dauka don shawo kan lamarin. Ya ce gwamnatin tarayya za ta cigaba da taimakawa.
A wani mummunan al'amari na nuna kiyayya ga al'ummar Yahudawa, wani bature dan akidar kyamar wasu jinsuna, mai su na Roberts Bowsers, ya hallaka yahudawa 11 a wata masujjadarsu a Amurka.
A wani yinkuri mai kama da dabarar samun karbuwa a kasar waje, jagoran 'yan awaren Biafra, Nnamdi Kanu, ya bulla kasar Isira'ila saye da hula da tufafin mabiya addinin Yahudu. Amma ya ce zai dawo Najeriya ya cigaba da fafatuka.
Kamar yadda ya zaba faruwa, an buga tsakanin 'yan sanda da direbobin motoci sakamakon lahanin da wasu 'yan sanda su ka yi ma wani direbo saboda wai ya ki ba su na goro. Wannan rigimar 'yan sanda da direbobi kan batun na goro ba bakuwa ba ce.
A wani yinkuri na karfafa gwiwar mata a Janhuriyar Nijar game da muhimmanci kwallon kafa, Amurka ta kuduri aniyar hada kai da Janhuriyra Nijar wajen inganta kwallon kafar mata, saboda su ma matan Janhuriyar NIjar a rika damawa da su a fagen wasan kwallon kafa, kamar yadda ake yi a sassan duniya.
Ga dukkan alamu hankula sun dada kwantawa a garin Kaduna - musamman ma a wusu unguwanni, al'amarin da ka iya kwadaita ma sauran unguwannin nuna halin son zaman lafiya saboda su ma a sassauta masu.
Hankali ya sake komawa kan irin namijin kokarin da matan karkara ke bayarwa musamman ma a fannin noma da tattalin arziki da zamantakewa.
Yayin da siyasa ke dada zafi saboda shirin zabe da ke tafe a 2019, wasu faya-fayen bidiyo sun bullo masu nuna kamar Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jahar Kano na amsar na goro daga wasu 'yan kwangila.
Domin Kari