Ana cigaba da taimaka ma mabukata albarkacin watan Ramadan.
Yayin da aka sace wani babban dan kasuwa a jahar Taraba, a jahar Adamawa kuwa damke masu aikata irin wannan danyan aikin aka yi
Wasu masu ibada a wani masallaci a Kano sun auna arziki bayan da wata yarinyar ta ake kyautata zaton 'yar kunar bakin wake ce ta tarwatse tun kafin ta kai ga masallacin.
Ganin yadda ake ta samun tashe-tashen hankula cikin 'yan kwanakin nan, shugabannin addinin Musulunci sun yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da sauran jama'a da a shiga addu'a da kuma hada kai wajen tona asirin miyagu.
Bayan wani dan lokaci na kwanciyar hankali a Jos, babban birnin jahar Filato, jiya da dare an kai wasu hare-haren bam biyu, wadanda su ka hallaka mutane.
Rashin bude bankuna a yankin Mubi da kewaye ya sa an shiga amfani da tsarin ba ni gishiri in ba ka manda a hadahadar cinakayya, al'amarin da ke cike da hadari
Yayin da ake ta kururuwar ta'azzarar sace mutane da shanu a jahar Naija, bayanai na nuna cewa 'yansanda sun yi hobbasa.
Wata kungiyar addinin Musulunci, SISAP a takaice, ta shirya wa mata lacca don karuwa a addinace da kuma zamantakewar yau da kullum.
Rikicin kungiyar gamayyar dillalun man fetur a Najeriya na neman wanzuwa da kuma kawo cikas ga tafiye-tafiye da kuma wadatar man a arewa maso gabas
Hukumomi sun bayyana fargabar cewa tashin hankalin da 'yan Boko Haram su ka jefa mutane a jahar Borno na janyo shayeshayen muggan kwayoyi don a huce.
Yayin da ake ta kokarin daukar matakan farfado da yankin Arewa Maso Gabashin Najeriya, Sanatocin yankin sun ce sun gana don gabatar da bukatar kafa hukumar farfado da yankin a Majalisar Tarayyar Najeriya.
Yayin da Hukumar Kwastam ta Kasa ke mika ma gwamnatin jahar Borno kayan tallafa ma 'yan gudun hijira a jihar, Gwamnatin ta Borno ta ce gwamnatin Jonathan ba ta yi wata rawar gani wajen tallafa ma ta ba
Duk da rashin samun isassun kayan agaji, wata kungiyar ba da tallafi ga marasa galihu ta yinkuro don raba abin da ya samu ga marayu.
Har yanzu ta na kasa ta na dabo dangane da zaben shugabannin Majalisar Tarayyar Najeriya. Amma APC ta ce ana gab da kawo karshen danbarwar.
Yayin da tashe-tashen hankula a sassan duniya ke kara yawan 'yan gudun hijira, an yi kiran da a tallafa masu, ganin yadda wahalarsu ke karuwa.
A wani cigaba a kokarin tabbar da zaman lafiya a Mali, 'yan tawayen Asbinawan Mali sun bi sahun wasu kungiyoyi wajen cimma jituwa da gwamnatin kasar
Kungiyar Ta'addar al-Shabab ta sake kai wani mummunan hari na ba-zata a Somaliya, kuma ana jayayya kan adadin wadanda abin ya rutsa da su - musamman daga bangaren sojin kasar.
Yayin da ake samun takaddama tsakanin bangarorin APC a jihar Adamawa, gwamnan jihar Sanata Muhammadu Bindow Jibrilla, ya ce shi bai da uban-gida; kuma da Atiku da Nyako duk iyayensa ne
Yayin da ake cigaba da kara bukatar taimaka ma wadanda rikicin Boko Haram ya rutsa da su a arewacin Najeriya, gwamnatin jihar Borno ta jinjina ma Amurka, tare da kiran a bi sahunta wajen bayar da tallafi.
Kwararru sun ce duk da ya ke 'yan Boko Haram na cigaba da kai hare-hare kamar yadda su ka saba, kashinsu ya kusa bushewa muddun Buhari na Shugaban Najeriya.
Domin Kari