Yayin da ranar zaben Nijeriya ke kara matsowa, hukumar zaben Nijeriya na kara jaddada cewa ta shirya tsab don gudanar da zaben, duk kuwa da nema a daga da wasu ke yi.
Ganin babban zaben Nijeriya ya kusatowa, 'yan Nijeriya na kara kiraye-kirayen a yi zabe da kyau kuma cikin adalci da gaskiya.
Boko Haram sun kai hari garin Fotokol na kasar Kamaru, to amma sojojin Chadi sun fatattake su.
Dan takarar Shugabancin Nijeriya karkashin jam'iyyar APC, Janar Muhammadu Buhari, wanda ya je yakin neman zabe a jihar Adamawa, ya ce lallai zai dau mataki kan jerin matsalolin da ke addabar Nijeriya.
Wani mai sharhi kan al'amuran yau da kullum ya lura cewa Kotun manyan laifuka ta kasa da kasa ka iya sa 'yan siyasa yin karatun ta natsu, ta wajen gargadi da kuma kashedin shirin daukar matakin da ya dace kan duk wani dan takarar da ya dayar da zaune tsaye.
Wani shugaban matasa ya ce ya kamata Nijeriya ta dubi kiran a kama jagoran tsageran Naija-Delta da idon basira
Ganin yadda siyasar Nijeriya ta shiga kasar Ghana har ake ta lillika hotuna da sakonnin kampe, jama'a da hukuma a Ghana, sun fara dari-dari, gudun abin da ka je ya zo.
An yi kiran da a yi adalci ga kowani dan Nijeriya da ya rasa waninsa ko dikiya a tashe-tashen hankulan kasar saboda a rage dumamar zamantakewa kafin zabe.
Darajar Naira dai na cigaba da faduwa saboda dalilan da kwararru su ka ce sun hada da faduwar farashin man fetur a duniya.
Ana kan zargin juna tsakanin gwamna Sule Lamido na jihar Jigawa da 'yan jam'iyyar APC musamman magoya bayan gwamna Aliyu Magatakarda Wamakko na jihar Sakkwato. Bangarorin biyu dai na zargin juna ne da butulci.
A yayin da wasu ke korafin rashin samun katin dindindin na zabe mai kara karatowa, ita ko hukumar zaben Nijeriya (INEC) ta ce kafin lokacin zaben za a warware duk wadannan matsalolin. Don haka ta shirya sosai.
Dan takarar Shugaban Nijeriya karkashin jam'iyyar APC kuma tsohon Shugaban Nijeriya Janar Muhammadu Buhari ya kare zargin da jam'iyyar PDP ta masa na rashin mallakar takardar shaidar kammala karatun Sakandare.
'Yan Boko Haram sun yi kokarin sake kwace garin Gombi dake jihar Adamawa.
Mai Martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi na Biyu ya yi kira ga Fulani da su rungumi al'adar da'a da zaman lafiya da kakansu Usman Dan Fodio ya gadar masu.
Shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan ya kai ziyara Maiduguri, babban birnin jihar Borno inda rikicin Boko Haram ya daidaita don gane ma kansa halin da ake ciki.
An cigaba da tarurrukan jaddada muhimmancin gudanar da zabukan 2015 cikin kwanciyar hankali.
Wani mai fashin baki ya ce da muhimmancin a tabbatar da 'yancin mutum da kuma na jarida kafada da kafada
A yayin da zabukan 2015 ke kara kusatowa, hukumar zaben Nijeriya ta ce ta daura damarar ganin cewa ba a yi magudi a zaben 2015 ba.
Yayin da zabukan 2015 ke kara matsowa, jam'iyyu na dada tallata alamominsu da manufofinsu.
Wani mai fashin baki ya bayyana kalaman Obasanjo na fifita Nijeriya kan duk wata jam'iyyar siyasa da cewa wani babban al'amari ne ganin matsayinsa
Domin Kari