Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC) ta ce ta shirya sosai don gudanar da zaben 2015. Ta kuma za a gudanar da zabuka a dukkannin wurare - har ma da inda ake da matsalar tsaro tunda a kasashe masu irin wadannan matsalolinma akan gudanar da zabuka.
Jihar Borno na fama da kwararar 'yan gudun hijira, baya ga matsalolin tsaron da ta ke fama da su, a cewa gwamna Kashim Shettima
A yayin da ake kara samun tashe-tashen bama-bamai a wuraren da jama'a su ka fai yawa, wani kamfanin tsaro da hukumar 'yan sandan Kano sun shirya bita ma 'yan kasuwa da sauran wadanda aka fai aunawa.
Shugabannin addinai da 'yan siyasa da sauran wadanda abin ya shafa sun yi taron jaddada muhimmancin gudanar da zabuka cikin lumana.
Hukumar Zaben Nijeriya (INEC) ta ce ta kammala gudanar da zabuka a jihar Naija; to amma fa ana ta korafi, musamman daga bangaren 'yan adawa.
Shugabannin addini da na kungiyoyi sun gardadi 'yan siyasa dangane da wajibcin tabbatar da zaman lafiya da kuma maido da 'yan matan Chibok.
Yayin da shirin zabukan 2015 ya fara zafi sosai, an shiga takaddama tsakanin PDP mai mulkin Nijeriya da babbar jam'iyyar adawa ta APC
A baya bayan nan, yinkurin kai hare-hare a Gombe ya kan ci tura ta yadda wani zubin ma dara ce kan ci gida. Ma'ana, 'yan kunar bakin wake sun yi ta tarwatsa kansu tun kafin su isa inda su ka nufa
Idan aka kula sosai za a iya gane yawancin wadanda ke dab da kai harin kunar bakin wake saboda alamomin fita hayyaci da kuma warin bakon turare ko magani.
Talakawa ma su na taka rawa wajen samar ma gwamnati sukunin taimaka masu ta wajen hada kai da tabbatar da kwanciyar hankali don hukuma ta yi aiki, in ji wani sheihin malamin jami'a.
Alhaji Balarabe Musa ya yi tir da yadda gwamnatocin siyasa a Nijeriya ya ce su kan kan dibi kudin jama'a su bai wa jam'iyyunsu su yi kampe.
A cigaba da bitar abubuwan da su ka auku a shekara mai shudewa, wani mai tsokaci kan al'amuran tsaro mai suna Dr. Bawa Wase ya yi kiran da a dau kwararan matakai don inganta tsaro na Nijeriya.
Manyan malaman addinin Kirista sun yi kiran da a yi koyi da Yesu Almasihu wajen yada zaman lafiya albarkacin lokacin Kirsimeti.
Hukumomin Tsaro a Jihar Kano sun bayyana ma jama'a yarinyar nan 'yar shekaru 13 da haihuwa, daya daga cikin kananan 'yan mata uku da aka tura su aikata harin kunar bakin wake a Kasuwar Kantin Kwari, wajen makonni biyu da su ka gabata.
Hukumar Tallafin Gaggawa Ta Birnin Tarayyar Nijeriya Abuja (FEMA) ta ce ya zuwa yanzu akwai akalla 'yan gudun hijira sama da 4,000 da ta ke kula da su. Kuma za ta tabbatar cewa miyagu basu saje da su sun addabi jama'a ba.
Rahotannin baya-bayan nan na nuna cewa adadin wadanda su ka mutu a hare-haren da aka kai Bauchi da Gombe 26 ne, banda wadanda su ka sami raunuka.
An kai hari kan wani bikin aure a Karamar Hukumar Gasol ta jihar Taraba, inda aka hallaka mutane 10.
Ana cigaba da yaba zaben Furfesa Yemi Osinbanjo Mataimakin Dan Takartar Shugabancin Nijeriya karkashin jam'iyyar APC.
Kwamitin Kula da addinai na rangadin bayyanawa addinai muhimmancin aiki tare da su don tabbatar da zaman lafiya a kasar
A yayin da farashin mai ke ta kara faduwa a kasuwannin duniya, Ministar Man Nijeriya Furfesa Okonjo Iweala ta gabatar da kasafin kudin 2015.
Domin Kari