Wani jigo cikin gungun wasu jiga-jigan 'yan PDP da su ka fishe daga jam'iyyarsu su ke kuma tunanin mataki na gaba, gwamnan jihar Kano Alhaji Rabiu Musa, ya ce su matakin da jama'a ke so za su dauka.
Ana samun cigaba a yaki da jahilcin da ake yi a jihar Kano; to amma akwai wasu matsaloli nan da can.
A kasar Burtaniya an yi bikin tunawa da rayuwar Bakar fata a Burtaniya na shekara shekara. Wannan karan an mai da hankali ne kan rawar da Burtaniya ta taka game da bauta.
Wani Kwararra a harkar zirga-zirgar jiragen sama kuma tsohon Sakatare-Janar na kungiyar masu harhar zirga-zirgar jiragen sama a Nijeriya mai suna keftin Muhammad Joji, ya ce ba a yi wa arewa adalci ba a kason zirga-zirgar jiragen sama a kasar.
Har yanzu ba a tantance ko su wa su ka kai hari garin Makarfi da daren Lahadi ba. Wasu na ganin 'yan fashi ne; wasu kuma na ganin 'yan Boko Haram ne.
An bayyana Tsayuwar Arafat a matsayin rukuni mafi girma cikin rukunonin aikin Hajji.
Hukumar Kula Da Zirga Zirgar Jiragen Sama ta Nijeriya ta dakatar da jiragen kamfanin DANA don gudanar da wani bincike.
Mahajjatan Nijeriya hudu sun rasu yayin da Hukumar Jin Dadin Alhazan Nijeriya ke ba da himma wajen kula da lafiyar Alhazan Nijeriya.
Sabanin yadda ta kasance a wasu jihohin Nijeriya, a jihar Oyo ta Kudu maso gabashin Nijeriya an yi bukukuwan ranar 'yancin Nijeriya.
Gwamnatin jihar Kano ta himmatu ga yaki da duk wata banzar dabi'ar da za ta iya hana jama'a, musamman ma matasa, amfana da ayyukan da gwamnati ke yi, in ji Kwamishiniyar Al'amuran mata.
Wasu manya a Nijeriya sun lura cewa muddun hukumomi da jama'a ba su sauke nauyin da ya rataya a wuyan su ba, sojoji ba za su iya tabbatar da zaman lafiya a Nijeriya ba.
Mummunar zangazangar adawa da janye tallafin man fetur na yaduwa a Sudan
Ana cigaba da zakulo gawarwaki da kuma farautar 'yan ta'addan al-Shabab a Kenya
Cibiyar Sasanta Jama'a Ta Kano mai samun taimako daga hukumar DFID ta Burtaniya ta yi nasarar sasanta jama'a da dama a Kano
Rikita-rikitar tsige Kakakin Majalisar Dokokin jihar Kaduna ta dau wani sabon launi. A yayin da Kakakin da aka ce an tsige ke jaddada cewa ya na nan daram, shi kuma sabon Kakakin har ya fara aikace-aikace.
Amirul Hajj na bana kuma Mai Martaba Shehun Borno ya gargadi maniyyata aikin Hajji tare da masu wasu muhimman bayanai.
Bangaren PDP da ya balle karkashin Alhaji Abubakar Kawu Baraje ya ce 'yansanda sun hana shi yin taronsa a otal din Awalah da ke Bauchi a karshen mako.
Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilan Nijeriya kan Zirga-zirgar kasa, Honorabul Musa Sarkin Adar yayi takaicin yadda gwamnatocin Nijeriya ke kin kammala ayyukan da su ka tarar, al’amarin da ya ce na janyo asarar kudi mai yawa da kuma hana jama’a amfana da ayyuka masu muhimmanci saboda kawai gwamnatin da ta shude ce ta fara.
Rigimar bangaranci a jam'iyyar PDP mai mulkin Nijeriya ta dau wani sabon salo, ta yadda sai da bangarorin su ka ba hammata iska a Majalisar Wakilan Nijeriya
'Yan Bangar da ake kira Fararen Hulan JTF sun yanka kunnen wani dan bindiga sun tilasta shi ya ci ya hadiye
Domin Kari