Wata dalibar jami'a ta maka masu ruwa da tsaki a yajin aikin da Kungiyar Malam Jami'o'in Nijeriya (ASUU) ke yi a kotu.
A karo na farko, wata na’urar jigilar sararin sama da dan adam ya kirkiro ta iya ficewa daga zangon duniyoyin da ke dogaro ga rana, da ake kira solar system
An bayyana 'yan Nijeriya da cewa masu karyar imani ne amma sai aikata masha'ar da ta hana kasar cigaba.
Hukumar Raya Kasashe ta Burtaniya, DFID a takaice, za ta cigaba da taimaka wa bangaren shari'ar jihar Kano
Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry ya ce goyon bayan kasa da kasa na karuwa kan bukatar a ladabtar da gwamnatin Siriya
Jami’an tsaron Misra sun ce a jiya Asabar an kashe tare da raunata wasu mutane da dama da ake kyautata zaton mayakan Islama ne
Yau Asabar ake zaben Shugaban kasa a kasar Australiya, inda ake ganin da kyar gwamnati mai ci ta su Firayim Minista Kevin Rudd ta kai labarai.
Shugaban Amurka Barack Obama ya ce yaki kawai ba zai magance matsalar Siriya ba. Sai an hada da hanyar siyasa.
Wani tashin hankalin da ya auku a jihar Naija ta arewacin Nijeriya ya yi sanadiyyar kona gidajen Fulani 36 da bacewar dabbobi wajen 70.
Gwamnatin Nijeriya ta tanaji daurin shekaru biyar ko tarar N200,000 ga duk wanda ya saba ma dokar WAEC
Paparoma Francis ya nada Ministan Harkokin Waje, mukamin da tamkar mataimaki ne gareshi
Shugaban Amurka Barack Obama na nemar amincewar Majalisar Tarayyar Amurka don kai hari Syria
Kungiyar Jama'atu Nasril Islam (JNI) ta ba da shawarar cewa a canza salon ayyukan tabbatar da tsaro a Nijeriya.
Wata makaranta mai zaman kanta da ke Borno na daukar nauyin marayu, musamman ma wadanda tashe-tashen hankulan yankin arewa maso gabashin kasar ya rutsa da su.
Dubun dubatan mutane ne su ka taro a Washington, babban birnin Amurka jiya Asabar don bukin zagayowar ranar jawabin Rev. Martin Luther King Jr.
Shugabannin kungiyar 'Yan'uwa Musulmi na fuskantar shari'a a kotu bisa zargin ingiza mummunar fitina
Hukumomin Duniya na cigaba da yin Allah wadai da munanan hare-haren da aka kai Lebanon.
Dubban magoya bayan kungiyar Ikhwanul Muslimin ta Misra sun yin zanga-zanga a fadin kasar jiya; amma yawansu da kuzarinsu ba su kai na baya ba
Hukumar Alhazan Nijeriya ta bayyana cewa ran 14 ga watan Satumban nan za a fara jigilar maniyyata aikin Hajjin bana.
Makafin jihar Naija sun koka da kama su da hukumomi ke yi don hana su bara ba tare da basu wani abu madadin barar ba.
Domin Kari