Shugaban kamfanin man fetur na Najeriya wato NNPC, Mele Kyari, ya bayyana cewa, kamfanin ba zai iya ci gaba da daukar nauyin biyan tallafin man fetur da ya ke yi don saukakawa ‘yan kasa farashin kowacce litar mai ba.
Rundunar ‘yan sanda a jihar Sokoto ta kama tare da tsare wani saurayi da budurwarsa da kuma wasu mutane akalla 5, da ake zargi da laifin kisan gilla ga wani Abba Abbey da ke unguwar Gidan Haki a tsakiyar birnin Sokoto.
Kungiyar ‘yan Canjin kudi ta yankin Arewa maso gabashin Najeriya ta bukaci a gaggauta sako mambobinta da hukumar tsaro ta farin kaya wato DSS ke tsare da su sama da mako biyu ba tare da wani sahihin bayanai akan laifin da suka aikata ba.
Attajirin dan kasuwa, Abdul Samad Rabiu mai kamfanin BUA ya kaddamar da wani shirin bada tallafin shekara-sheara na dala miliyan 100 na nahiyar Afirka wanda aka yiwa lakabi da “Shirin tallafin Abdul Samad Rabiu, don ci gaban zamantakewar jama'a.”
Najeriya ta dakatar da zirga-zirgar kamfanin jiragen saman Emirates zuwa cikin kasar, bayan da ya kakabawa fasinjoji ‘yan Najeriyar dokar karin matakan gwajin cutar coronavirus.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da harin da wasu ‘yan bindiga suka kai wa ayarin gwamnan jihar Benue Samuel Ortom, amma kuma ya yi gargadin ka da a mayar da lamarin siyasa.
Tsohon shugaban mulkin soji na Najeriya Yakubu Gowon, ya yi kiran da a bi tsarin shugabancin kasar na karba-karba a tsakanin manyan yankuna 6 na kasar.
Gwamnan babban bankin Najeriya wato CBN, Godwin Emefiele, ya ce tsarin tattalin arzikin fasahar zamani na da muhimmanci matuka, a kokarin da gwamnatin tarayya ke yi na kawo ci gaba a dukan fannoni a cikin shekaru masu zuwa.
Babban bankin Najeriya ya sanya harajin Naira 6 da kwabo 98 kan hada-hadar kudi ta na’ura ga ‘yan kasar, wanda hakan ke nufin masu asusun bankuna zasu rinka biyan Naira 6 da kwabo 98 a duk lokacin da suka yi hada-hadar kudi ta na’ura ko wayan tarho daga ranar 16 ga watan Maris da muke ciki.
Majalisar Matasan Najeriya (NYCN), ta yi kira ga shugaban kasar Muhammadu Buhari, da ya gaggauta ayyana ‘yan bindiga masu garkuwa mutane a fadin kasar a matsayin ‘yan ta’adda.
'Yan bindiga sun yi awon gaba da daliban kwalejin horar da harkokin noma da lamurran da suka shafi gandun daji ta gwamnatin tarayyya da ke unguwar Mando a cikin birnin Kaduna.
Gwamnan jihar Zamfara Bello Muhammad Matawalle ya ce ayukan ta’addanci da ‘yan bindiga ke yi a jihar ba su da alaka da hakar ma’adanai musamman zinari da ake yi a wasu sassan jihar.
Sarkin masarautar Anka na jihar Zamfara, Attahiru Ahmad, ya bayyana cewa, ‘yan bindiga dadi sun yi garkuwa da masu hakar ma’adinai sama da 100 da ke aiki tsakanin kananan hukumomin Anka da Marun a ranar 2 ga watan Maris da mu ke ciki.
Gwamnatin Najeriya ta ba da umarnin kara tsaurara matakan tsaro a filayen jiragen sama da ke Arewacin kasar, biyo bayan wani farmaki da wasu ‘yan bindiga suka kai a filin jirgin saman kasa-da-kasa na Kaduna, inda suka yi awon gaba da wasu ma’aikatan filin jirgin.
Kungiyar mayakan Boko Haram ta sako Pastor Bulus Yikura, sa’o’i 24 kafin wa’adin da kungiyar ta bayar na kashe shi.
Hukumar lafiya matakin farko ta Najeriya wato NPHCDA, ta kawar da fargabar yiyuwar ‘yan kasar ba za su so a yi musu allurar rigakafin cutar Korona birus ba.
Mayakan Boko Haram da ba a tantance adadin su ba sun fice daga garin Dikwa kafin isowar sojoji bayan kwashe tsawon sa’o’i suna rike da iko a garin tare da hana shige da fice.
‘Yan bindiga sun kai hari a kauyuka 3 da ke cikin kananan hukumomin mulkin Igabi da Kajuru na jihar Kaduna, inda suka kashe mutane 7.
‘Yan sanda a kasar Spain sun kai samame a kungiyar kwallon kafar Barcelona, inda suka kama wasu manyan jami’an kungiyar Oscar Grau, da kuma Roman Gomez Ponti, jagoran lauyoyin kungiyar.
Sabuwar babban daraktar hukumar kasuwanci ta duniya wato WTO, Dr. Ngozi Okonjo-Iweala, za ta fara aiki gadan-gadan a hukumar yau litinin 1 ga watan Maris, Shekarar 2021.
Domin Kari