‘Yan bindiga sun saki yaran makarantar sakandaren kimiyar gwamnati ta Kagara da ke karamar hukumar mulkin Rafi ta jihar Neja.
Kungiyar Dattawan Arewa ta yi kira ga malamin addinin Musulunci Sheikh Ahmad Gumi da ya gaggauta dakatar da ziyarar da yake yi a sansanonin 'yan ta'adda.
Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da adadin ‘yan mata dalibai da aka sace a makarantar sakandaren Jangebe da sanyin safiyar yau Juma’a.
‘Yan bindiga a jihar Zamfara da ke Arewacin Najeriya sun kai farmaki a wata makarantar sakandaren 'yan mata da ke garin Jangebe a karamar hukumar mulkin Talata Mafara, inda suka yi awon gaba da daliban makarantar.
Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya bayyana sace ‘yan matan makarantar sakandaren Jangebe a jihar Zamfara a matsayin take hakki da 'yancin yara.
Hadakar kungiyoyin masu fataucin kayan abinci da dabbobi musamman daga Arewa zuwa Kudancin Najeriya, ta fara yajin aikin sai baba ta gani a fadin kasar.
Hadakar kungiyoyin arewa ta sake jaddada goyon bayanta ga yunkurin sulhunta rikici tsakanin gwamnati da 'yan bindiga da Sheikh Gumi ke yi.
Kwamitin jin Korafin Jama'a na Majalisar Waklilan Najeriya ya sake gayyatar mai kwarmato Dr. George Uboh kan bahasi na zambar kudin shiga sama da dala biliyan 25 daga kamfanonin man kasashen ketare.
Ana ci gaba da cacar baki tsakanin gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed da takwaransa na jihar Benue Samuel Ortom dangane da sha’anin Fulani makiyaya, duk kuwa da sa baki da jam’iyyarsu ta PDP ta yi.
‘Yan bindiga sun saki mutane 53 da suka sace a jihar Naija da ke Arewacin Najeriya, to amma ban da dalibai 27 na makarantar sakandare ta Kagara, da wasu murtane 15 da aka yi awon gaba da su a makon jiya.
Dan wasan gaba na kungiyar Crystal Palace Wilfried Zaha ya ce zai daina gurfanawa a gwiwarsa kamar yadda ake yi kafin buga kowace wasan gasar Premier, domin karfafa fafutukar “Rayuwar Bakar Fata na da Muhimmanci.”
Kungiyar kwallon kafar Manchester City ta Ingila ta nisanta kan ta da rahotannin da ake bazawa, da ke ta’allaka ta da zawarcin shahararren dan wasan Barcelona ta kasar Spain, Lionel Messi.
Sahararren dan wasan kasar Portugal da ke taka leda a kungiyar Juventus ta kasar Italiya Cristiano Ronaldo ya kamu da cutar coronavirus.
Matashin dan wasan Ingila da kungiyar Manchester United Marcus Rashford ya sami lambar karramawa ta MBE ta masarautar Britaniya, sakamakon kokarin da yayi na taimakawa iyalai masu karamin karfi.
Dan wasan Najeriya da ke taka leda a kungiyar Chelsea ta Ingila Victor Moses, na kan hanyar barin kungiyar zuwa kungiyar Spartak Moscow ta kasar Rasha a zaman aro na tsawon kakar wasanni.
Ma'aikatar lafiya ta jahar Filato da ke Arewacin Najeriya ta ce ta samo wata sabuwar dabarar yaki da cutar coronavirus a jihar.
Masana tattalin arziki sun fara yin fashin baki akan kasafin kudin shekara mai zuwa ta 2021, da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatarwa majalisar dokokin kasar.
Duk da yake shugaban Amurka Donald Trump na fuskantar koma baya a kuru’un jin ra’ayoyin jama'a, to amma ya na ci gaba da samun goyon baya a yankunan karkara. inda manoma suke kuma suka samu taimakon da gwamnati ta yiwa sashen noma.
Muhawara da aka tafka tsakanin mataimakan 'Yan takarar Shugaban kasar Amurka da ta kasance daya tilo da zasu yi kafin zaben shugaban kasa, ta tabo batutuwa da dama da suke sosawa Amurka rai.
Hukumar kwallon kafar Najeriya - NFF, ta nada dan kasar Amurka, Randy Waldrum, a matsayin mai horar da tawagar ‘yan wasanta mata na Super Falcons.
Domin Kari