Sai dai hukumar Kwastam ta bakin kakakinta ta musanta yin ba daidaiba a harkokin fansar da gwanjan kaya.
Sai dai hukumar ta kwastam ta musanta wannan zargi tana mai cewa dukkan ayyukan da take yi da suka shafi gwanjon kaya, ana yin su ne bisa ka'ida.
Shirin ya ta'allaka ne kan rikicin rushewa wasu mutane gininsu da suka ce an yi a jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya.
An yi kira ga gwamnatin tarayyar Najeriya da ta saki Mazi Nnamdi Kanu madugun kungiyar IPOB, da ke fafutukar kafa kasar Biafra, bayan kotu ta wanke shi.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a jawabinsa a taron majalisar dinkin duniyar a nan New York, ya yabawa kasashe masu hulda da Najeriya bisa goyon bayansu ga harkokin zabe a kasar, sannan ya yi Allah wadai da shugabannin da suke kin mutunta wa’adin mulkinsu, da wasu rahotanni
Bayan bayyana sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a kasar Kenya, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya taya William Ruto, murnar lashe zaben.
Tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ce jami'an hukumar binciken manyan laifuka ta FBI sun kai samame a gidansa na Mar-a-Lago da ke Palm Beach a jihar Florida.
Shugaban Amurka Joe Biden ya sanar da cewa, an kashe shugaban kungiyar Al Qaeda Ayman al-Zawahiri a wani harin da hukumar leken asiri ta CIA ta kai a Afganistan a karshen mako, wanda shi ne tashin hankali mafi girma ga kungiyar tun bayan kashe wanda ya kafa kungiyar Osama bin Laden a shekarar 2011.
Masu kamfanoni da masana’antu a Najeriya suna kokawa da hauhawar farashin hatsi, musamman alkama, sakamakon yakin da Rasha ke yi da Ukraine, da wasu rahotanni
Domin Kari