Accessibility links

Har Yanzu Babu Adadi na Wadanda Suka Mutu Ko Suka ji Rauni a Harin Bam Biyu a Maiduguri

  • Garba Suleiman

Mutane suna gudu yayin da hayaki ke shiga cikin samaniya bayan da bom ya fashe a inda sojoji ke girke a garin Maiduguri, Janairu 14, 2014.

A bayan da mutane suka taru domin taimakawa wadanda bam na farko ya rutsa da su, sai na biyun ya tashi ya hallaka, ya raunata wadanda suka je taimako.

Har yanzu, ba a samu adadin farko na yawan mutanen da suka mutu ko suka ji rauni a hare-haren bam guda biyu da aka kai da motocin daukar itace a Maiduguri, cibiyar kungiyar nan ta Boko Haram ba.

Shaidu na gani da ido sun ce da misalin maghariba ta asabar din nan ce bam na farko ya tashi, inda aka ga mutane jina-jina sun a ta gudu ta ko ina, yayin da hayaki ke tashi daga wurin. Wani dan tireda da ake kira Sama’ila, yace bam din ya tarwatsa wasu mutanen baki daya.

Bam na biyu ya tashi ya rutsa da mutanen da suka je domin taimakon wadanda suka ji rauni a tashin bam na farko a wannan unguwa mai suna Bintu-Suga a wata gundumar da ake kira Ngomari.

Dan tiredan yace da alamun bam din an dana ne a cikin wata motar a kori-kura ta daukar itace, wadda kuma aka zuba itace a kan duk abinda ke boye a kasa cikinta.
Mallam Sama’ila yace, “Ina ganin mutane suna ta wucewa da gawarwaki jina-jina. Akwai gabobin mutane warwatse ta ko ina a kan titi.”

Wani makaniki mai suna Yahaya Adamu, yace yana kan hanyarsa ta zuwa gida sai ya ji tashin bam din, kuma bayan minti biyu sai ya ji tashin wani bam din kuma. Yace ya ga bakin hayaki ya tashi sama, sai kuma ya garzaya zuwa gida domin tabbatar da cewa iyalinsa suna nan kalau.

Wannan shi ne harin farko da aka kai cikin watanni a Maiduguri, hedkwatar Jihar Borno, kuma cibiyar rundunar sojojin da aka damkawa alhakin murkushe kungiyar nan ta Boko Haram wadda ta yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane a cikin shekaru hudu da fara tawaye.

An kashe mutane fiye da 300 a watan da ya kare na Fabrairu, dukkansu a jihohin Yobe da Adamawa makwabtan Borno.

Ana kara nuna fusata da yadda sojoji suka kasa kawo karshen irin wadannan hare-haren, inda aka bayarda rahotannin cewa sojojin dake kula da wasu wuraren tsarewa da binciken mutane da ababen hawa sun gudu daga wuraren aikin nasu a lokutan wasu hare-haren da suka kashe mutane kusan 100, ciki har da wasu dalibai 59. An ce dalili shi ne tsagera ‘yan bindigar sun fi su yawa da kuma makamai.
XS
SM
MD
LG