Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasuwa: Hada-hadar Kasuwanci a Kasuwar Garki Village, Abuja, Mayu 22, 2022


Yayin da ake hada-hadar sayen kayan masarufi a wata kasuwa a Kano

Shirin Kasuwa na wannan makon ya kai ziyara kasuwar Garki Village da ke Abuja, babban birnin Tarayyar Najeriya.

Washington, DC - Wakilin muryar Amurka Saleh Shehu Ashaka ya yi hira da ‘yan kasuwar ta Garki Village da suka bayyana masa farashin kayayyaki a yanzu da kuma lokutan baya.

Galibi ‘yan kasuwar sun bayyana cewa farashin kayayyaki ya karu sosai a yanzu.

Wata mai saida tuwon shinkafa a kasuwar mai suna Hajiya Asabe Hussaini, ‘yar asalin jihar Nasarawa, wadda ta kwashe kusan shekara talatin tana sana’ar, ta ce babu yadda farashin abincinta bai kamawa saboda unguwar da take.

Saurari cikakken shirin cikin sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:10:00 0:00

XS
SM
MD
LG