Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abin Da Masana Shari'a Ke Cewa Kan Hukuncin Da Kotu Ta Yankewa Farouk Lawal


Tsohon dan majalisa Farouk Lawal.

Lauyoyi a Kano da masu sharhi kan harkokin yau da kullum, musamman a fagen siyasan Najeriya na ci gaba da yin fashin baki dangane da hukuncin babbar kotun tarayya na daurin shekaru 19 ga tsohon dan majalisar wakilai Faruk Lawal.

A ranar Talata kotun ta zartar da hukuncin ga tsohon ‘dan majalisar saboda samun sa da laifin karbar toshiyar baki a shekarar ta 2012 daga Femi Otedola, wanda dan kasuwa ne mai hada-hadar albarkatun mai, domin ya wanke ko cire kamfaninsa daga jerin kamfanonin da gwamnati ke zargi da almundahanar kudaden albarkatun mai.

Shekaru 19 kotun ta yanke wa tsohon dan majalisar akan laifuka guda 3 da aka tuhume shi da su, amma daga baya suka rikide suka zama 7.

A cewar Dr. Nasiru Adamu Aliyu SAN lauya ne mai zaman kansa a Kano, laifukan a jere da kwanakin ne aka yi lissafinsu daga karshe kotun ta bada hukuncin shekaru 7 a jere maimakon 19.

Karin bayani akan: Farouk Lawal, Nigeria, da Najeriya.

Sai dai Dr. Sa’idu Ahmad Dukawa na Jami’ar Bayero, Kano ya yi tsokaci ne akan makomar laifin da aka zargi Mr. Femi Atedola na cin amanar dukiyar kasa.

Ya kuma yi bayani cewa Farouk Lawal ya nema karbar kudin ne domin ya kama Otedola amma bai san cewa shiga Otedola ya yi niyyar kama Farouk Lawal saboda tambayar da ya yi masa ta kudin domin cire sunan kamfaninsa. Ya ce amma Daga karshe Faruk ne aka kama.

Ga alama dai lauyoyi da alkalai za su ci gaba da fafatawa akan wannan batu, domin kuwa ta yiwu Hon. Faruk Lawan zai daukaka kara zuwa kotu ta gaba.

Saurari rahoto cikin sauti daga Mahmud Ibrahim Kwari:

Abin Da Masana Shari'a Ke Cewa Kan Hukuncin Da Kotu Ta Yankewa Farouk Lawal
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:09 0:00


XS
SM
MD
LG