Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abuja: Litinin Ce Ranar Afirka Domin Karrama Hadin Kai


Taron koli na shugabannin Afirka karo na 50th.

Kungiyar Hadakan Kasashen Afirka Ta Taka Rawargani, ko yaya, ra'ayi dai ya banbanta.

Abuja-Yau take ranar Afirka Ana wannan bukin ne duk shekara domin tunawa da kuma karrama ranar da aka kafa kungiyar hada kan kasashen Afirka da aka fi sani da sunan OAU a takaice. An kafa kungiyar ranar 25 ga watan Mayu 1963.

An kafa wannan kungiyar ce da zummar habaka tattalin arziki, da kiwon lafiya, da tsaro da ci gaban al'uma. Shekaru 52 bayan kafuwarta akwai wadanda suke yaba ayyukanta da irin nasarori data samu, akwai kuma wadanda suke ganin kungiyar bata taka rawar azo a gani ba.

Masu sukar lamirin kungiyar suna bada misali da irin rigingimu na cikin gida a kasashe kamar 'yar autawar kungiyar-Sudan ta kudu, da Burundi, da Somalia, da Angola da kuma a Najeriya, inda rikicin Boko Haram ya galabaitar da arewa maso gabashin kasar. Yanzu rikicin ya shafi kasashe makwabtan Najeriya, da suka hada da Cadi, da Nijar, da kamaru.

Amma a nasa bangaren tsohon shugaban Zanzibar Amani Karumi yace gaskiya kungiyar ta taka rawar gani sosai. Yace wadansu rigingimun suna aukuwa kwatsam ba zato ba tsammani.

Ga karin bayani.

Abuja-Yau Take Ranar Afirka-Domin Karrama Kafa Kungiyar Hada Kan Kasashen Afirka - 3'18"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:18 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG