Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adadin Sarakunan Gargajiya Da 'Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa Da Su A Najeriya


‘Yan Bindiga
‘Yan Bindiga

Sama da sarakuna dari da goma sha uku ne ‘yan bindiga suka yi garkuwa dasu a sassa daban-daban na Najeriya cikin shekaru hudu da suka shige. Yayin da kuma wasunsu ma suka rasa rayukansu hade da hadimansu.

Amma cikin wannan shekara da muke bankwana da ita ta 2021, a wani yanayi na kara tabarbarewar tsaron, yan bindigar na kara maida hankali wajen sace sarakunan.

Garkuwa Da Sarakuna A Najeriya
Garkuwa Da Sarakuna A Najeriya

A zancen da ake yanzu haka ‘yan ta'addan na can naci gaba da yin garkuwa da mai martaba Sarkin Gindiri a jihar Filato har sun tuntubi masarautar suna neman kudin fansa.

Hakanan ma a jihar Imo inda ‘yan bindigar ke gasar sace sarakunan don yin garkuwa dasu, a halin yanzu suna rike da wani babban Badarake.

To ko me yaja hankalin ‘yan ta'addan na afkawa iyayen kasa? Wani masani a jami'ar Abuja, Dr. Faruk BB Faruk na jami'ar Abuja yace ta yiwu ganin masu garkuwan sun san sarakunan na da ni’ima da daraja a wurin mutane da dama wannan ya sa in sun kame su za ayi maza a harhada masu kudin da suke nema.

Kudin Fansa
Kudin Fansa

Air Commodore Baba Gamawa shi kuwa cewa yayi dole ne fa gwamnati ta tashi haikan wajen ganin ta murkushe yadda ake ta sace-sacen mutane haka barkatai, in ba haka ba to ba shakka sai masifar ta hadiye kowa sannu a hankali.

Tun tuni dai masana tsaro irinsu Manjo Janar Yakubu Usman ke kokawa ganin yadda kullum ake kama masu satar mutanen a nuna su ga ‘yan jarida daga nan sai aji shiru, yana mai cewa muddin ana hukunta masu laifin to hakan zai rage barnar.

‘Yan Bindiga
‘Yan Bindiga

To amma ‘yan sanda na cewa suna kama masu laifin in sun gudanar da bincike kuma su kaisu kotu daga nan sun gama nasu.

Saurari rahoto cikin sauti daga Hassan Maina Karina:

Ana Ci Gaba Da Yin Garkuwa Da Sarakunan Gargajiya A Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:52 0:00


Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG