Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Amince A Dauki Sabbin ‘Yan sanda Dubu 10 A Aiki


'Yan sandan Najeriya (Facebook/Rundunar 'yan sandan Najeriya)
'Yan sandan Najeriya (Facebook/Rundunar 'yan sandan Najeriya)

Daukan karin ‘yan sandan a aiki na zuwa ne yayin da Najeriyar ke fuskantar matsalolin tsaro a wasu yankunanta.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ba da umarnin a dauki sabbin ‘yan sanda dubu 10,000 a kasar.

Mai taimakawa Buhari a fannin yada labarai ta kafafen zamani Bashir Ahmad ne ya bayyana hakan cikin wani sako da ya wallafa.

“Shugaba Muhammadu Buhari ya ba da umarnin a dauki ‘yan sanda 10,000 a matsayin jami’an ‘yan sanda a jihohi 36 da babban birnin tarayyar Abuja.” Ahmad ya ce.

An dauki wannan mataki ne, “don a tunkari kalubalen tsaro a wasu sassan kasar.”

A cewar sanarwar, an dauki mutum 10 ne a kowace karamar hukuma cikin kananan hukumomi 774 da ke Najeriya, kuma tuni har an sanar da wadanda aka dauka ta hanyar emel da suka nemi aikin.

Daukan karin ‘yan sanda a aiki na zuwa ne yayin da Najeriya ke fuskantar matsalolin tsaro a sassanta.

A Arewa maso yammacin kasar na fama da ‘yan fashin daji da ke kai hare-hare da sace mutane domin neman kudin fansa.

Arewa maso gabashi kuma tana fama da matsalar Boko Haram da ISWAP, yayin da a kudu maso gabashin kasar take fama da matsalar ‘yan awaren kungiyar IPOB.

XS
SM
MD
LG