Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akwai Yuyuwar Najeriya To Mika Abba Kyari Ya Fuskanci Hukumci - Malami


Atoni Janar din Najeriya, Abubakar Malami, hagu, Abba Kyari, dama (Facebook/Instagram/Malami/Kyari)
Atoni Janar din Najeriya, Abubakar Malami, hagu, Abba Kyari, dama (Facebook/Instagram/Malami/Kyari)

Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, SAN, a jiya, ya bayyana cewa an kafa wata shari’a ta farko a kan mataimakin kwamishinan ‘yan sandan da aka dakatar Abba Kyari kan zargin zamba da gwamnatin Amurka ta yi masa da ya shafi wani mutum mai damfarar yanar gizo, Hushpuppi.

A wata hira da gidan Talabijin na Channels, Malami ya bayyana cewa akwai wasu hukunce-hukuncen shari’a a cikin lamarin da suka hada da Hadaddiyar Daular Larabawa, Amurka, da Najeriya. Malami ya bayyana cewa, “Akwai abubuwa da dama da ake tafkawa, ciki har da yiwuwar mika shi, kuma shi ya sa bangaren hadin gwiwar ya shigo, ana iya samun bukatar a mika shi.

Malami ya ce: “Hukumomi da dama suna da hannu a ciki. Don haka, a yanayin da ake ciki, kasashen duniya suna yin komai don tabbatar da an yi adalci a lamarin.

Ministan shari’ar Abubakar Malami ya ce akwai abun zargi da su ka fahimta kan rahoton tuhumar dan sanda Abba Kyari da hannu kan zamba cikin aminci na miliyoyin dala.

Malami bai ce kai tsaye Abba Kyari ya aikata laifi ba, amma akwai tabbacin abun zargi game da shi da zai saka a iya daukar matakan shari’a ko mika shi Amurka don a can ne a ke gudanar da shari’ar.

Bayan kammala binciken ta, rundunar ‘yan sandan Najeriya dai gwamnati ba ta bayyana sakamakon abun da tagano ba.

In za a tuna a bara hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka ta zargi Abba Kyari a laifin damfarar da ya shafi babban dan damfarar nan Ramon Abbas da a ka fi sani da Hushpuppi da a yanzu haka ya ke jiran yanke ma sa hukunci a Amurka.

Malami ya kuma yi tsokaci kan batun masu tallafawa ta’addanci tare da tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa babu wani abu da za a boye game da bayyana sunayensu, da hujjojin da ke tattare da su.

XS
SM
MD
LG