Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akwatunan Talibijan da Basu da Tsarin Zamani ba Zasu Shiga Najeriya


Talibijan
Talibijan

Sabili da daidaita harkokin sadarwa su zama daya da na duniya hukumar sadarwar Najeriya ko NBC a takaice tana shirin dakatar da shigowa da akwatunan talibijan da basu da tsarin zamani

Hukumar sadarwa ta Najeriya ta kudiri dakatar da shigowa da akwatunan talibijan da basu da tsarin zamani.

Hukumar ta dauki matakin ne daidai lokacin da take shirin daidaita shirye-shiryen talibijan su zo daidai da na zamani kamar sauran kasashen duniya. Shugaban hukumar Emeka Mba shi ya bayyana hakan lokacin da yake kaddamar da kwamiti mai mutane 13. Ya ce za'a fara gwajin anfani da tsarin zamanin ne a gidan talibijan da radiyo mallakar jihar Filato.

Mr. Emeka Mba ya ce duk da cewa shirin ka iya karo da matsaloli yana da karfin gwiwar cewa shirin zai ci nasara ganin yadda gwamnatin tarayya ta dauki shirin da mahimmanci. Ya ce mutanen Jos sun samu wata dama ce ta musamman a ta yadda za'a sauya harakar talibijan ta kasance da inganci da yadda za'a rika cudanya a kuma samu anfani masu dimbin yawa.

Kwamishanan yada labarai ta jihar Filato Madam Olivia Dazem ta jaddada goyon bayan gwamnatin Filato wajen ganin shirin ya samu karbuwa. Sakataren kwamitin Abdulkadiri Abubakar Kurawa ya ce tsarin zamanin masu akwatunan talibijan na yanzu ba zasu iya kama gidan talibijan ba sai suna da naurar da zata sauya masu wato abun da ake kira converter a turance muddin basu da akwatin talibijan da yake da tsarin zamani. Ya ce babu wani kudi da za'a dorawa mutum ya biya sai dai ya sayi ita converter din. Taimakon da zasu iya yi a hukumance shi ne su yi tsarin da zai takaita farashen converter.

Aikin da aka dorawa kwamitin shi ne ya fito da adadin kudin da za'a kashe domin aikin ya mike. Abu na biyu shi ne ilmantar da jama'a kan sabon shirin domin kamar a jihar Filato mutane da yawa basu san za'a koma wani sabon shiri ba.

Shi kuma janaral manajan gidan talibijan da radiyo manllakar jihar Filato ya ce sun shirya tsaf su soma sabon shirin. Gwamna ya riga ya saya masu kayan na zamani wadanda ake bukatansu domin sabon sauyin.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:06 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG