Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Alhazan Najeriya Ta Cimma Yarjejeniya da Hukumomin Saudiya


Alhazai sun taru kusa da birnin Makka

Kamar shekarar da ta gabata hukumomin Saudiya sun amince su baiwa Najeriya kujerun alhazai 76,000

Aikin hajin bana kamar bara maniyatta 76,000 ne zasu samu zuwa kasa mai tsarki daga Najeriya.

Babban jami'in kula da harkokin kafofin labarai na hukumar alhazan Najeriya Alhaji Uba Mana ya zanta da wakilin Muryar Amurka kan shirin aikin hajin bana da dalilin da ya sa a wannan shekarar ma kamar bara kujeru 76,000 aka baiwa Najeriya. Ya ce takaita kujerun daidai da na bara ya biyo bayan ayyukan da har yanzu ana yi ne a can kasa mai tsarki. To amma da zara an kammala ayyukan da ake yi yanzu Najeriya na iya samun kari fiye da 95,000 da aka saba bata kafin soma ayyukan da ake yi yanzu. Idan ba'a manta ba kasar Saudiya ta rage kashi 20 na duk maniyatta daga kasashen duniya bara kuma haka ta kasance a wannan shekarar.

Dangane da wasu alhazai da suka ki dawowa gida da kuma wadanda ake kora daga kasar Alhaji Uba Mana ya ce sun tabo irin wadan nan matsalolin da hukumomin Saudiya. Kodayake akwai mutane daga kasashe da yawa a Saudiya idan basu da takardun zama dole a komar da su kasashensu. To amma yawanci 'yan Najeriya na samun matsaloli ne saboda rashin sanin yaren da dokokin kasar. Ya ce kafin a farga sai jami'an Saudiya su kulle 'yan Najeriya. To irin wadan nan matsalolin sun tattauna a kansu tare da hukumomin Saudiya. Ya ce idan alhaji ya samu matsala hukumomin Saudiya basa sanarda hukumar alhazai ko ofishin jakadancin Najeriya. Ya ce sun kai kuka kuma sun amince cewa bai kamata a kama maniyattan Najeriya ba kuma a ki sanarda hukumarsu ko ofishin jakadancin Najeriya. Sabo da haka bisa ga yarjejeniyar nan gaba ko an kama wani alhaji za'a sanarda hukumar ko ofishin jakadancin Najeriya.

Ita ma hukumar ta ce a nata bangaren zata yi kokari ta wayar da kawunan maniyatta da sanarda da su abubuwan da ya kamata su kula da su da wadanda yakamata su kiyaye. Koda ma mutum ya yi laifi akwai hukuma akwai kuma ofishin jakadanci da yakamata a sanar da su.

Tun da babu kari a kujerun bana yakamata jihohi su fara shiri kan yadda aka basu bara sai dai jihohin da suka yi laifi ana rage masu alhazai. Duk jihar da take da laifi ba zata samu adadin kujerun da ta samu bara ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:22 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG