Lamarin ya farune yayin da koguna suka balle tare da cika tituna a karshen mako, kamar yadda kafafen yada labarai na kasar suka ruwaito a ranar Litinin.
Hotunan kafar yada labaran kasar SABC sun nuna yadda motoci ke kokarin bi ta magudanan ruwa da suka mamaye manyan tituna.
Kafofin yada labarai da dama sun ba da rahoton cewa ruwan ya wuce da daruruwan gidaje a matsugunan rufin karfe da ke wajen birnin, musamman a garin Mdantsane.
Masana kimiya na zargin cewa sauyin yanayi ne ya janyo ambaliyar ruwa da fari a gabar tekun gabashin kasar, a birnin ke da mutane kusan rabin miliyan.
-Reuters