Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Aminu Hassan Gamawa Ya Ce Babu Dalilin Yin Murna


Rashin tsaro na daga cikin dalilan hana 'yan Najeriya yin murnar ranar 'yancin kai inji Aminu Hassan Gamawa.
Rashin tsaro na daga cikin dalilan hana 'yan Najeriya yin murnar ranar 'yancin kai inji Aminu Hassan Gamawa.

Aminu Hassan Gamawa yace yanzu ba mulkin mallaka ake yi ba, amma duk manufofin shugabannin kasar domin su dad'ad'awa turawa ne

Albarkacin cikon shekaru hamsin da uku da samun 'yancin kan kasar Najeriya Halima Djimrao ta tattauna da Lauya Aminu Hassan Gamawa na jami'ar Harvard ta nan Amurka, inda ya duba al'amarin kasar Najeriya daga wancan lokaci ya zuwa yanzu ya ce ci gaban da aka samu bai amfani talakan kasar Najeriyar ba. Lauya Aminu Hassan Gamawa ya fara da bayyana mahimmacin samun 'yancin kai ga kowace kasa da kuma kowace al'umma, amma ya ce su dai 'yan kasar Najeriya ba su da wani kwakkwaran dalilin yin murnar cikon shekaru hamsin da uku da samun 'yancin kai.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:23 0:00
Shiga Kai Tsaye
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG