Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Bada Izinin Amfani Da Allurar Pfizer Ga Yan Shekaru 12 Zuwa 15


coranvirus vaccine

Hukumar kula da ingancin magunguna ta Amurka ta ba da izini ga kamfanin Pfizer da BioNTech na amfani da allurar rigakafin COVID-19 ga yara ƙanana daga shekaru 12 zuwa 15.

An samu isashen allurar rigakafin a ƙarƙashin izinin yin amfanin gaggawa ko kuma (EUA) ga yara ƙanana daga shekaru 16 a Amurka. Masu samar da rigakafin sun ce sun fara aikin ne don samun cikakkiyar amincewa ga masu wadandan shekarun a makon da ya gabata.

Kira Lundell, 16, who is on the autism spectrum, receives a coronavirus disease (COVID-19) vaccine at Variety - the Children’s Charity of the Delaware Valley.
Kira Lundell, 16, who is on the autism spectrum, receives a coronavirus disease (COVID-19) vaccine at Variety - the Children’s Charity of the Delaware Valley.

Hukumar Abinci da Magunguna ta Amurka ta ce za ta yi gyara a tsarin don ta hada da miliyoyin yara ‘yan shekara 12 zuwa 15.

Wannan ita ce allurar rigakafin COVID-19 ta farko da aka ba da izini a Amurka don wannan rukunin shekarun, wanda ake gani a matsayin muhimmin mataki don dawo da yara makarantu lafiya.

Shugaban Amurka Joe Biden ya nemi jihohi da su hanzarta samar da isashen allurar rigakafin ga kananan yara.

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG