Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Sami Zinari Na Farko A Gasar Olympic


Red Gerard dan wasan tseren dusar kankara

Wani matashi Ba'amurke da ya shiga gasar Olympic karon farko ya sami zinari

Wani matashi ya samarwa Amurka lambar yabo ta farko a gasar Opympic da ake gudanarwa a PyeongChang, inda ya sami zinari.

Matashin dan shekaru goma sha bakwai Red Gerard, daga Silverthorne, jihar Colorado, wanda karon farko ke nan yake zuwa wasan Olympic, ya sami zinarin ne a gasar wasan tseren kan dusar kankara ta maza.

Gerard ya doke abokan fafatawarsa 'yan kasar Canada ne a karon karshe Max Parrot wanda ya sami azurfa, da kuma Mark McMorris wanda ya sami tagulla karo na biyu bayan gasar Sochi shekaru hudu da suka shige.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG