Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Zata Ci Gaba Da Jan Kunnen Iran Kan Makaman Nukiliya


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

A yau litinin Amurka za ta saka takunkumi akan mutane fiye da 24 da wadanda ke da hannu a shirin nukiliya da makamai masu linzami na Iran.

Wani babban jami’i da yake karfafa takunkumin Majalisar Dinkin Duniya a kan Tehran, shi ne ya bayyana haka, inda Washington ta ce ta dawo da takunkumin, duk da kin amincewar wasu kawayenta da magoya bayanta.

Da yake Magana bisa sharadin a sakaya sunan sa, Jami’in ya ce, Iran za ta tanadi sinadarai na kera makaman nukiliya a karshen shekara kuma Tehran ta shiga yarjejeniyar makamai masu cin nisan zango da Kasar Koriya ta Arewa. Amma bai ba da cikakkiyar shida akan haka ba.

Sabon Takunkumin ya yi daidai da kokarin shugaban Amurka Donald Trump na takaita tasirin da Iran ke da shi a nahiyar, kuma yana zuwa ne mako guda bayan da Amurka ta cimma yarjejeniyar daidaita alaka takanin hadaddiyar Daular Larabawa da Bahrain da Izraila.

Gwamnatin Trump na zargin Iran da neman makaman nukiliya, batun da Tehran ta musanta kuma matakan na ranar Litinin za su kasance sabon kokarin dakushe shirin Iran na samar da makaman nukiliya, wanda ke barazana ga Amurka da kawayenta.

Wani jami’in Amurka da ya tattauna da kamfanin dillancin labaran Reuters, ya ce Iran tana so ta mallaki makamin nukiliya kana ta yi amfani da makamin, duk da yarjejeniyar shekarar 2015 da ta haramta mata yin haka, ta hanyar takaita shirinta na makaman atomic, inda ita kuma Iran zata samu damar shiga kasuwar duniya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG