Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Zata Hana 'Yan Sudan Bizar Shiga Kasar Ta


Mike Pompeo
Mike Pompeo

Gwamnatin Amurka ta sanar a wannan mako cewa zata fara hana bada biza ga mutanen dake katsalandan ga gwamnatin farar hula ta kasar Sudan. Umarni zai shafi jami’an tsohuwar gwamnatin shugaba Omar al Bashir da aka hambarar da ita da wasu da dama, inji sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo.

Gwamnatin Trump zata aiwatar da haramta bada biza a karkashin dokar bakin haure da zama dan kasa a kan daidaikum mutane dake zaune a ciki da wajen kasar Sudan da ake sa ran suna da hannu ko kuma suna shirya katsalandan ga kokarin da gwamnati ke yi na aiwatar da yarjejeniyar siyasa ta ranar 17 ga watan Yulin shekarar 2019 da kuma shirin ayyana kundin tsarin mulki na ranar 17 ga watan Agustan 2019 a cewar sanarwar.

Daidaikun mutane da aka samu su da cin hanci da rashawa ko kuma cin zarafin ‘yan kasa, su kuma za a hana musu bizar Amurka, a cewar Pompeo.

Karamar jakadiyar Sudan a Amurka, Amira Agarib, ta yi marhabi da wannan matakin.

“Mun dauki wannan shawara a matsayin mataki mai inganci, hakan kuma na nuni da alakar mu da Amurka na yin kyau kuma muna samun nasara wurin fitar da Sudan a cikin jerin kasashen dake taimakawa ayyukan ta’addanci, inji Agarib tana fadawa shirin South Sudan in Focus na Muryar Amurka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG